An Kama Masu Garkuwa kan Sace 'Yar Shekara 1, Aka Wurga Ta Rijiya a Kano, Abba Ya Magantu
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana jin dadinsa kan yadda DSS ta kama mutane da ake zargi da garkuwa da kuma kisan wata yarinya
- Wadanda ake zargin duk 'yan unguwar Duhun Bake ne kuma sun karbi kudin fansa sannan suka kashe yarinyar suka jefar da gawarta a rijiya
- Gwamnatin Kano ta bayyana aniyar hukunta wadanda ke aikata laifuffuka tare da karfafa tsaro da hadin gwiwar hukumomin tsaro a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa hukumar DSS bisa yadda ta gaggauta kama wasu mutum biyar da ake zargi da aikata garkuwa da kisan gilla.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sun yi wa wata karamar yarinya mai suna Sakina Mamuda kisan gilla a unguwar Duhun Bake, karamar hukumar Gwarzo.

Asali: Facebook
Bisa ga sanarwar da Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a Facebook, wadanda ake zargin sun sace Sakina ne sannan suka nemi kudin fansa kafin daga bisani su kashe ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu gawar yarinyar a cikin wata rijiya da aka daina amfani da ita, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma musamman mazauna yankin.
Wadanda ake zargi da kisan yarinya a Kano
Sanarwar ta bayyana sunayen wadanda aka kama da hannu dumu-dumu da laifin kamar haka: Zailani Rabiu, Hafizu Yusuf, Abubakar Abdulkareem, Umar Lawan da kuma Amadu Salisu.
Dukkan su daga unguwar Duhun Bake su ke, inda abin ya faru, kuma ana ci gaba da bincike a kansu kan laifin hada baki, garkuwa da mutane da kuma kisan kai.
Gwamnatin Abba ta yi alkawarin daukar mataki
A taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano, kwamishinan shari’a na jihar, Barista Haruna Isa Dederi ya ce za a dauki mataki kan lamarin.
An yi taron ne tare da kwamishinan yada labarai da wasu manyan jami’an gwamnati, inda suka bayyana cewar gwamnati ba za ta lamunci irin wannan danyen aiki ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna alhini bisa wannan aika-aikar tare da yaba wa DSS da sauran jami’an tsaro bisa daukar mataki cikin gaggawa.

Asali: Facebook
Ya kuma ce gwamnati za ta kara ba da kulawa na musamman a bangaren tattara bayanan sirri da hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.
Kiran Abba ga jama'a da hukumomin tsaro
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafa wa dukkan hukumomin tsaro da kayan aiki da goyon baya domin tabbatar da tsaron al’umma.
Haka kuma, ya bukaci al’umma da su kasance masu bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro domin saukaka gano masu laifi cikin lokaci.
Lamari dai ya janyo fushin jama’a tare da kira da a gurfanar da wadanda ake zargi da hukunta su cikin gaggawa.
An kama wanda ya kashe mahaifinsa a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'ya sandan jihar Jigawa ta kama wani matashi da ake zargi da kashe mahaifinsa.
An kama matashin ne a wata unguwa a garin Sara da ke karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa.
Kakakin 'yan sandan jihar, Shi'isu Adam Lawal ya bayyanawa Legit cewa za a gurfanar da wanda ake zargin da zarar an kammala bincike.
Asali: Legit.ng