Sheikh Gumi Ya Kare Kansa da Aka Tsoma Shi a Matsalar Sace Dalibai a Oyo
- Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana game da neman tsoma shi cikin lamarin sace dalibai da aka yi a wata makaranta a jihar Oyo
- Gumi ya bayyana cewa bai je Ibadan bisa gayyatar Musulman Kudu maso Yamma ba, illa wakiltar malaman Musulunci na Arewa
- Malamin ya danganta sukar da aka yi masa da siyasar tsoron Musulunci, yana goyon bayan MURIC kan batun shari'ar Oyo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya yi martani kan ziyarar da ya kai Ibadan a ƙarshen shekarar da ta gabata.
Wannan na zuwa ne bayan wasu sun nuna fushi tare da zargin cewa yana ƙoƙarin yaɗa wasu akidu da koyarwar Arewa a Oyo.

Source: Facebook
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata 9 ga watan Yunin 2026, ya ce ya je Ibadan ne a madadin gamayyar malaman Musulunci na Arewa.

Kara karanta wannan
Kungiyar dattawan Arewa ta yi wa Tinubu, Kwankwaso, Atiku, Obi kudin goro kan zaben 2027
Shiekh Gumi ya fadi dalilin kai ziyara Ibadan
Gumi ya jaddada cewa babu wanda zai hana shi ziyartar ko ina a cikin Najeriya, domin ƙasar ta kowa ce.
Ya kuma bayyana cewa babu wata ƙungiyar Musulmi ko wani mutum daga Kudu maso Yamma da ya gayyace shi.
Ya bayyana hakan ne kwana guda bayan ɗaya daga cikin mutanen da aka sace a Oriire ya musanta zargin neman kafa shari'a a Oyo.
Legit Hausa ta ruwaito cewa shugabar makarantar 'Community High School', Esiele, Misis Rachael Alamu, ta yi magana daga hannun masu garkuwa.
A cikin bidiyon da ya bazu, ta ce masu garkuwar ba su nemi kafa shari'a ko a biya kudin fansar Naira biliyan ɗaya ba, ta ce sun bukaci sako abokan hulɗarsu ne kawai.

Source: Original
MURIC tana goyon bayan Sheikh Gumi
Hakazalika, ƙungiyar Muslim Rights Concern (MURIC) ta yi watsi da rahoton neman kafa shari'a a wata sanarwa da ta fitar.
MURIC ta bayyana rahoton a matsayin "ƙarya", tana zargin maƙiyan Musulunci da ƙirƙirar labarin.
Da yake goyon bayan matsayar ƙungiyar, Gumi ya ce yanzu ya fahimci yadda tsoron Musulunci ke tasiri a siyasar Kudu maso Yamma.
A cewar Gumi:
"Na je Ibadan ba bisa gayyatar wani Musulmi ko wata ƙungiyar Musulmi ta Kudu maso Yamma ba.
"Na je ne a matsayin wakilin gamayyar malaman Musulunci na Arewa. Shin akwai wanda zai hana ni zuwa ko'ina a Najeriya?"
A ranar 19 ga Nuwamban 2025, Gumi ya kai ziyara Ibadan inda ya kasance babban bako kuma mai jawabi.
Taron ya gudana ne a Jami'ar Ibadan a matsayin Babban Taron Malaman Musulunci na Kudancin Najeriya.
Gumi ya sake neman afuwa ga yan bindiga
Mun ba ku labarin cewa Ahmad Gumi ya bukaci Gwamnatin tarayya ta yi wa ‘yan bindiga afuwa kamar yadda aka yi wa tsofaffin mayaƙan Boko Haram.
Malamin ya ce amfani da ƙarfin soji kaɗai bai kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta shafe akalla shekaru 17 ana addabar jama'a da kashe rayuka.
Sheikh Ahmad Gumi ya musanta zarge-zargen cewa yana goyon bayan ta’addanci ko ayyukan ‘yan bindiga da ke addabar talakawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
