Kotu ta daure shugaban karamar hukuma a gidan yari

Kotu ta daure shugaban karamar hukuma a gidan yari

Wani alkalin kotun majistri ya kama daure shugaban karamar hukumar Buruku ta jihar Benuwe mai suna David Yiman.

Kotu ta daure shugaban karamar hukuma a gidan yari

David Yiman shine sabon shugaban hukumar da gwamnan jihar Samuel Ortom ya nada a ranar 11 ga watan Oktoba, an daure shi tare da Kosuvenyi Kungwa da Emmanuel Nyajo kan zarginsu da aikata laifin kisan kai.

Yansanda sun kama mutanen uku ne kan zarginsu da kisan wani malamin jami’ar Mkar Aondosso Wilfred mai shekaru 50 wanda jaridar Punch ta ruwaito cewa an kashe malamin ne a watan Agusta 2016. Ana zargin mutanen ne da hadin baki tare da wasu mutane uku wajen yin kisan.

KU KARANTA: Mata sun yi garkuwa da sakataren gwamnatin jihar Delta

Sai dai a zaman kotun na farko, ba’a saurari korafin da wasu suka shigar na kalubalantar hurumin alkalin na sauraren karar. Lauyan hukumar yansanda Hyacenth Mbakwor yace haryanzu ba’a kammala binciken lamarin ba. Daga nan sai ya bukaci kotu da ta dage sauraron karar zuwa wani rana na daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng