Sojojin Iran Sun Saki Bama Bamai kan Amurka bayan Harin Trump a Tehran
- Rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce ta kai hare-hare kan wurare 21 na sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya
- Kasar Iran ta sanar da cewa hare-haren sun shafi Bahrain da kuma Jordan, yayin da rundunar sojin Kuwait ta ce ita ma ta dakile wani hari
- Hare-haren kasar Iran sun biyo bayan ceto ma’aikatan jirgin sama biyu na jirgin Amurka da aka harbo a kusa da mashigar Hormuz
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Rahotanni sun nuna cewa rundunar Iran ta IRGC ta kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka a Bahrain, Kuwait da Jordan.
Iran ta bayana cewa hare-haren na ramuwar gayya ne kan harin da Amurka ta kai kan tashoshin jiragen ruwa da tsibirai na Tehran da ke mashigar Hormuz.

Source: Getty Images
Wuraren Amuka da Iran ta farmaka
Al Jazeera ta rahoto cewa IRGC ta ce ta kai hare-haren jiragen sama marasa matuka kan rundunar ruwan Amurka da ke Bahrain da kuma sansanin jiragen sama na Ali Al Salem da ke Kuwait, tare da sansanin jiragen sama a Azraq da ke Jordan.
Iran ta ce ta kai hari kan wurare 21 na Amurka tare da lalata hudu daga cikinsu, ciki har da wurin ajiye jiragen yaki na F-35 a sansanin da ke Jordan.
Haka kuma ta yi ikirarin harbo wani jirgin sama maras matuki na Amurka kirar MQ-9 a sararin samaniyar birnin Jam na Iran.
Sabon tashin hankalin ya zo ne bayan sojojin Amurka sun kai hari kan tsibirin Qeshm da tashoshin jiragen ruwa da ke gabar tekun Iran a mashigin Hormuz bayan sun zargi Iran da harbo wani jirgin helikwafta na Apache.
Iran ta gargadi cewa dakarunta suna cikin cikakken shiri don mayar da martani ga duk wani matakin soji da Amurka za ta dauka.
An kunna kararrawa a kasar Bahrain
A Jordan, rundunar sojin kasar ta ce ta tare tare da harbo makamai masu linzami biyar da aka harbo daga Iran zuwa Azraq, tana mai cewa aikin ya haifar da fadowar tarkace ba tare da jikkata mutane ko lalata dukiya ba.

Source: Getty Images
Rahoton Times of India ya nuna cewa hare-haren sun sa an kunna kararrawar gargadin hare-haren sama a Bahrain da Kuwait.
Tun da farko rundunar sojin Kuwait ta ce tana dakile harin abokan gaba ta sararin samaniya a cikin kasar, ba tare da karin bayani ba.
Trump ya gargadi Netanyahu
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya gargadi Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu a wata tattaunawa ta waya game da sake komawa yaki da Iran.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Litinin Trump ya gaya wa Netanyahu cewa idan ya koma yaki da Iran, zai iya samun kansa yana fada shi kadai ba tare da gudunmuwar Amurka ba.
Iran da Isra’ila sun shiga wata babbar arangama a karon farko tun bayan ayyana tsagaita wuta a watan Afrilun 2026 amma sun dakatar da hare-haren bayan rokon da Trump ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

