Babban Malamin Musulunci, Sheikh Dawud Ya Rasu a Jihar Bauchi

Babban Malamin Musulunci, Sheikh Dawud Ya Rasu a Jihar Bauchi

  • An sanar da rasuwar babban malamin Musulunci, Sheikh Dawud Muhammad a jihar Bauchi bayan shafe shekaru yana yi wa addini hidima
  • Rahotanni sun nuna cewa a yau Laraba, 10 ga Yunin 2026 za a gudanar da jana'izar shi, inda aka bukaci jama'a su hallara domin masa addu'a
  • Malamai da dama a fadin Najeriya sun bayyana wasu abubuwa da suka sani game da Sheikh Dawud Muhammad tare da rokon Allah ya ji kan shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Kungiyar Izala ta jihar Bauchi ta sanar da rasuwar Sheikh Dawud Muhammad a ranar Talata, 9 ga watan Yunin shekarar 2026.

Rahotanni sun nuna cewa malamin yana cikin wadanda suka shafe shekaru suna yi wa addini hidima tun lokacin da aka kafa kungiyar Izala.

Kara karanta wannan

Alwashin sojojin Najeriya, Amurka kan tsaro bayan hare hare sun karu a Kudu da Arewa

Sheikh Dawud Muhammad
Sheikh Dawud Muhammad da ya rasu a Bauchi. Hoto: Ibrahim Disina
Source: Facebook

Shafin kungiyar Izala da ke jihar Bauchi ne ya wallafa sanarwar rasuwar Sheikh Dawud Muhammad a wani sako da ta fitar a Facebook.

Yaushe ne jana'izar Sheikh Dawud Muhammad?

Kungiyar Izala ta bayyana cewa a yau Laraba za a yi wa marigayi Sheikh Dawud Muhammad jana'iza a masallacin Gwallaga da ke Bauchi.

Sanarwar ta ce:

"Ana sanar da daukacin al'umma cewa Allah ya yi wa babban malaminmu, Sheikh Dawud Muhammad rasuwa. Za a gudanar da sallar jana'izarsa ranar Laraba da misalin karfe 10:00 na safe a babban masallacin Juma'a na Gwallaga, Bauchi."

Bayanin Dr Ibrahim Disina

Shugaban Sunnah TV, Dr Ibrahim Disina ya wallafa a shafin shi na Facebook cewa marigayin ne na farko-farko cikin 'yan agajin Izala.

Dr Disina ya wallafa cewa:

"Su ne 'yan agajin farko a Izala a Bauchi! Da furfurarsa su ne kan gaba a majlisin Malam Ja'afar a Bauchi!
"Su ne Manyan Jagorori a Tafsirin Farfesa Muhammad Sani Rijiyar Lemo a Bauchi.

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: Shugaban Izala a Kebbi ya rasa ransa a hannun 'yan bindiga

"Shi Malam Ja'afar ya sanar masa cewa na samu karatu a Madina ya sanar da ni.
"Kullum kowace sallah yana masallacin Gwallaga!!"

Sakon ta'aziyyar Farfesa Sani Rijiyar Lemo

Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya fitar da sakon ta'aziyya yana jimamin rasuwar Sheikh Dawud a shafinsa na Facebook.

Ya ce:

"Allah ya ji kan Malam Dawud ya karbi kyawawan ayyukansa, ya yafe masa kurakurensa, ya sanya Aljanna ce makomarsa, ya kula da bayansa. Amin."
Sheikh Sani Rijiyar Lemo
Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo. Hoto: Office Of Sheikh Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo
Source: Facebook

Ta'aziyyar Dr Jalo Jalingo

Shugaban malaman kungiyar Izala na kasa, Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya yi alhinin rasuwar marigayin a wani sako da ya fitar a Facebook.

"Muna roƙon Allah maɗaukakin sarki ya gafarta wa Sheikh Dawud Muhammad Bauchi.
"Muna miƙa ta'aziyyarmu da ban haƙurinmu ga dukkan Iyalansa masu daraja. Muna miƙa ta'aziyyarmu ga shugaban ƙungiya na ƙasa Sheikh Abdullah Bala Lau."

Malam Abubakar Pharmacy ya rasu

A wani labarin, mun kawo muku cewa matashin malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Malam Abubakar Pharmacy ya rasu.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya kare kansa da aka tsoma shi a matsalar sace dalibai a Oyo

Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa matashin malamin ya rasu ne bayan fama da jinya mai tsanani da ya yi.

Na kusa da marigayin sun sanar da cewa ya rasu ne a jihar Kano kuma a can aka yi masa jana'iza bayan kai shi jihar asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng