Dubun Wasu Rikakkun 'Yan Fashi da Makami Ta Cika a Jihar Adamawa

Dubun Wasu Rikakkun 'Yan Fashi da Makami Ta Cika a Jihar Adamawa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da aikata fashi da makami a garin Yola
  • Ana zargin daya daga cikin mutanen da hada baki da wasu wajen yin fashin makudan kudi da kuma kayyaki daga wani shago
  • Wani da ake zargin dan kungiyar Shilla ne ya shiga hannu bayan da ya sari wani mutum da adda tare da yi masa fashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Adamawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta sanar da cafke wasu mutum biyu da ake zargi da aikata fashi da makami a karamar hukumar Yola ta Arewa.

Kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 9 ga watan Yunin 2026.

'Yan sanda sun cafke 'yan fashi da makami a Adamawa
Taswirar jihar Adamawa, inda 'yan sanda suka cafke 'yan fashi da makami. Hoto: Legit.ng
Source: Original

‘Yan sanda sun cafke 'yan fashi a Adamawa

Kara karanta wannan

Yadda miji da mata suka tafka damfarar kusan N2bn da matakin da EFCC ta dauka

SP Nguroje ya ce jami’an ‘yan sanda da ke aiki a ofishin rundunar na Doubeli ne suka kama mutanen bisa zargin hannu a wasu laifuffuka daban-daban, in ji rahoton Punch.

Sanarwar ta bayyana cewa a ranar 3 ga watan Yunin 2026, jami’an ‘yan sanda sun kama wani matashi mai suna Idris Auwal mai shekaru 22 da ke zaune a yankin Doubeli Culvert da ke Yola ta Arewa.

A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa Idris ya hada baki da wasu mutum uku da har yanzu ake nema, inda suka yi fashi a wani shago da ke Nassarawo Borehole mallakin Abdullahi Sunusi.

An ce wadanda ake zargin sun yi awon gaba da jaka dauke da makudan kudi, muhimman takardu da kuma kayayyakin shago.

An kwace makamai da waya

Rundunar ta ce bayan gudanar da bincike mai zurfi an samu nasarar cafke Idris Auwal yayin da ake ci gaba da neman sauran wadanda suka tsere.

A wani lamari makamancin haka, rundunar ta ce jami’an ‘yan sanda na Doubeli sun sake kama wani da ake zargin dan kungiyar Shilla ne a ranar 5 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya kare kansa da aka tsoma shi a matsalar sace dalibai a Oyo

Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya tare wani mutum mai suna Abubakar Abdullahi a hanyar Doubeli Bypass dauke da adda, inda ya yi masa fashin wayar salula kirar Itel da kuma kudi N19,000.

An kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya jikkata mutumin a kai da adda kafin jami’an ‘yan sanda su isa wurin cikin gaggawa su kama shi.

'Yan sanda sun sha alwashin yaki da kungiyar 'yan Shilla a Adamawa.
Dakarun rundunar 'yan sanda na yaki da ayyukan ta'addanci za su fita aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda za su yaki da kungiyar Shilla

SP Nguroje ya ce ana ci gaba da bincike kan wadanda aka kama yayin da jami’ai ke kokarin cafke sauran mambobin kungiyar Shilla da suka tsere, in ji rahoton The Guardian.

Ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa za ta ci gaba da yaki da ayyukan kungiyar Shilla da sauran nau’o’in laifuffuka.

Rundunar ta kuma bukaci mazauna jihar su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Sojoji sun dura kan 'yan fashi

A wani labari, mun ruwaito cewa, sojoji sun dakile harin fashi da makami a babbar hanyar Abuja–Kaduna ba tare da asarar ran matafiya ko na jami'ai ba.

Kara karanta wannan

Dakarun 'yan sanda sun kutsa dajin Zamfara, sun yi gaba da gaba da 'yan bindiga

Rundunar ta ceto matafiya tare da kama wani daga cikin ’yan fashin bayan an yi gumurzu a lokacin da aka samu labarin harin.

Rundunar sojojin Najeriya ta sake jaddada aniyarta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kira ga ’yan ƙasa da su rika ba wa hukumomin tsaro bayanai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com