'Yan Bindiga Sun Tarwatsa Kasuwa a Filato, Sun Sace Mutane da Kayayyaki

'Yan Bindiga Sun Tarwatsa Kasuwa a Filato, Sun Sace Mutane da Kayayyaki

  • Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kasuwa a yankin Dogon Ruwa da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato, inda suka sace mutane biyar a ranar Litinin
  • Shaidu sun bayyana cewa maharan sun shigo cikin kasuwar ne a babura, inda suka fara harbe-harbe wanda ya jefa jama’a cikin firgici da guje-guje
  • Baya ga sace mutane, ‘yan bindigar sun fasa shaguna, sun kwashe kayan abinci da magunguna, lamarin da ya kara jefa al’ummar yankin cikin tsoro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro, musamman a Arewacin ƙasar da rikicin ‘yan bindiga ke ta’azzara.

A karamar hukumar Wase ta jihar Filato, wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a kasuwar Dogon Ruwa, inda suka sace ‘yan kasuwa biyar a safiyar jiya Litinin.

Caleb
Yan ta'adda sun kai hari cikin kasuwa a jihar Filato. Hoto: The Government of Plateau State
Asali: Facebook

Rahotan Channel TV ya tabbatar da cewa harin ya auku ne a daidai lokacin da kasuwar ke cike da jama’a daga kauyuka daban-daban da suka zo gudanar da harkokin kasuwanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun bude wuta a kasuwar Filato

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun shigo cikin kasuwar ne a kan babura da dama, inda suka bude wuta ba kakkautawa.

Wani mai shago, Abdullahi Isma’il, ya bayyana cewa maharan sun zagaye kauyen kafin suka nufi kasuwa, inda suka dauki wasu ‘yan kasuwa biyar suka tafi da su.

Rahoton Radio Najeriya ya nuna cewa dan kasuwar ya ce:

“Sun zo da yawa, wasu daga cikinsu suka nufi kai kasuwar kai tsaye suka dauki ‘yan kasuwa guda biyar.
"Muna ganin sun yi niyyar kai harin ne saboda yau ce ranar kasuwa domin su kwashi kayan abinci,”

An kwashi kayan abinci a kasuwar Filato

Baya ga sace mutane, ‘yan bindigar sun fasa shaguna da dama, inda suka kwashi kayan abinci kamar shinkafa, wake, fulawa, da sauran kayan masarufi, tare da daukar magunguna.

Dogon Ruwa dai na daga cikin manyan kasuwannin yankin, inda ‘yan kasuwa da masu sayayya daga kauyuka da dama ke haduwa duk mako domin gudanar da kasuwanci.

caleb
Harin kasuwa ya kara dagula matsalar tsaro a Filato. Hoto: The Government of Plateau State
Asali: Twitter

Wannan hari ya kara tayar da hankali a tsakanin mazauna yankin da suka dade suna fama da hare-haren ‘yan bindiga a yankin Bashar da kewaye.

Harin ya kara dagula lamarin tsaro

Al’ummar Wase da wasu sassan Filato sun shafe watanni suna cikin hali na rashin tabbas, inda aka kashe mutane da dama, wasu kuma suka rasa muhallansu sakamakon hare-hare.

Harin na Litinin ya sake jaddada bukatar daukar matakin gaggawa daga hukumomi domin kawo karshen ta’addancin da ke kara dagula rayuwar jama’a a yankin.

Rikici a Filato tun a baya

An dade ana fama da matsalolin tsaro a jihar Filato, musamman a sassan Kudu da Gabas kamar Wase, Barkin Ladi, Riyom da Bassa.

Tun kusan shekara goma sha da suka wuce, yankin ya kasance cikin rikici da tashe-tashen hankula, wanda galibi ya samo asali daga rikicin makiyaya da manoma, rikicin kabilanci da na addini.

Wannan ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi da dama tare da raba dubban mutane da muhallansu.

Yankin Wase da ke fama da sabon harin ‘yan bindiga, na daga cikin wuraren da ke fama da matsalar tsaro na tsawon lokaci.

Ana kai farmaki a kauyuka da kasuwanni, inda jama'a ke fuskantar sace-sace, fasa shaguna da kwace dukiya. Wannan ya janyo tsoro da durkushewar harkokin tattalin arziki, musamman kasuwanci da noma.

Kowanne lokaci da hare-haren ke faruwa, al’umma na kara rasa yarda da ikon gwamnati wajen kare rayuka da dukiyarsu.

Duk da irin kokarin hukumomi da jami’an tsaro ke yi, harin da aka kai kasuwar Dogon Ruwa ya sake nuna cewa matsalar tsaro a Filato ba sabuwa ba ce, kuma tana bukatar sabbin hanyoyi na magance ta.

'Yan bindiga sun kai hari a Benue

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ba a gane ko su waye ba sun kai zafafafan hare hare jihar Benue.

Wani rahoto ya nuna cewa 'yan ta'addan sun kai harin ne dauke da manyan makamai suka kashe mutane da dama.

Legit ta rahoto cewa 'yan bindigar da suka kai harin sun bi wasu mutane har gida sun kashe su har lahira yayin da suka yi ta'addancin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng