'Na Fa Fuskar Yarinyata,' Makahon da Ya Shekara 27 Babu Idanu Ya Dawo Yana Gani

'Na Fa Fuskar Yarinyata,' Makahon da Ya Shekara 27 Babu Idanu Ya Dawo Yana Gani

  • Rabon da idanun Abdullahi Abubakar su yi aiki shekaru 27 kenan, sai yanzu da aka yi masa aiki a asibiti
  • A wannan tattaunawa, ya bayyana yadda ya rayu cikin makanta da irin wahalhalun da ya fuskanta a rayuwa
  • Abdullahi ya kuma bayyana halin da yake ciki a yau da ya samu yake gani bayan likitoci sun gyara jijiyoyinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Abdullahi Abubakar ya shafe shekaru 27 yana rayuwa bai gani a sakamakon makanta da ta kashe masa idanu tun tuni.

An haife shi a jihar Kebbi, amma ya girma a Wudil da ke jihar Kano, matashin ya rasa ganinsa yana da shekaru uku a duniya.

makaho
Abdullahi Makaho da ya dawo yana gani da hoton sandar wani makaho Hoto: Getty Images
Source: UGC

Hirar da aka yi da wanda ya zama makaho

A hirarsa da Daily Trust, ya bayyana cewa a tsawon rayuwarsa, ya fuskanci wariya saboda makanta da yake fama da ita.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya sake maganganu kan Atiku, ya tono tsohon tarihi

Abdullahi Abubakar ya sha wahalar neman abin da zai ci. Ya dogara da abokansa wajen zirga-zirga da harkokin yau da kullum.

Sai dai makonni bakwai da suka gabata, an yi masa aiki a asibitin kwararru na Makkah Specialists Eye Hospital a Kano.

An yi masa aikin a asibitin ne sakamakon cututtukan glaucoma da optic neuritis da suka shafi idanunsa da jijiyoyin gani.

An yi masa tambaya game da yadda rayuwarsa ta kasance kafin tiyatar da aka yi masa.

Ya ce:

Mun je asibitoci da dama, amma ba a samu nasarar magani ba. Daga baya, na hakura da neman magani, na karbi kaddarata.
Makanta na zuwa da kalubale da dama. Ko a gida ma, ana iya daukar mutum a matsayin wanda ba shi da amfani, sai dai a ciyar da shi da kula da shi.
Ya ce yana da abokai da suke taimaka mini wajen kai ni wuraren da nake son zuwa.

Kara karanta wannan

Akpabio: Kiristan dan siyasa ya tura dubban Musulmi Makkah a masa a addu'a

Ya ce:

"Amma ban karaya ba. Na karanci ilimin addinin Musulunci, sannan na gwada sana'o'i daban-daban domin bana son rokon mutane."

Matashin ya ya yi karatu saboda ya ce bai son ya zama mabaraci. Ya yi sana’ar ga-ruwa, cinikin dabbobi amma daga karshe dole ya rika rokon jama’a.

Yaushe aka yi masa aikin idon?

Ya bada labari:

"Yanzu mako na bakwai kenan bayan tiyatar. Likitoci sun gano ina fama da cututtukan glaucoma da optic neuritis.

Da aka tambaye shi, ‘ya yaya ka rasa ganinka?’, sai ya ce:

Na fara fama da matsalar ne ina da kusan shekaru uku. Saboda ina karami sosai, ba zan iya tuna yadda abin ya faru ba.
Na shafe shekaru 27 ina makanta. Yanzu ina da shekaru 30.

Yadda aka yi masa aiki a asibitin Makkah

A baya, ya gwada magunguna a asibitoci daban-daban. Sau da yawa, ana fada masa cewa ba zai samu lafiya ba sai ya je kasar waje an duba shi.

Kara karanta wannan

2027: Dattijon Arewa da ya yi siyasa da Sardauna ya yi maganganu kan Tinubu

"Daga nan na hakura da neman magani. An shafe shekaru tara ana kokarin nemo maganin matsalar.
"Kwanan nan, wani makwabcinmu dan sanda ya kai ni wani asibiti a Kano. Bayan an yi min gwaje-gwaje, likitoci sun ce akwai yiwuwar dawo mini da gani, amma ana bukatar tiyata a jijiyoyin gani.
"Sun ce za a kashe N180,000. Ba ni da kudin, don haka na nemi taimako daga wajen ’yan uwa da abokai, amma ban samu nasarar tara kudin ba."

- Abdullahi

Ya ce shugaban karamar hukumar Wudil ya biya kudin da aka yi masa aiki ya dawo yana gani

Ya ce:

"Daga nan muka je asibitin Makkah Specialists Eye Hospital da ke Kano. Likitoci sun tabbatar da cewa akwai yiwuwar tiyatar ta yi nasara."

Me ya fara gani bayan idanun sun dawo?

Ya ce an fara tiyatar da misalin karfe 8:00 na safe. An yi aiki a kan idon da jijiyoyin gani, sannan aka rufe shi da bandeji da aka kammala.

"Da zarar an kammala, na fara ganin alamun haske. Daga nan aka rufe min idon da bandeji.

Kara karanta wannan

Kisan Ayatollah Ali Khamenei ya damu Trump, ya nuna alamun nadama

"Washegari, lokacin da aka cire bandejin, na ga wani haske mai karfi har na kasa kallonsa sosai.
"Likitoci sun daga yatsa guda suka tambaye ni yawan yatsun da nake gani. Na ce na san lambobi ne kawai, ban saba gani da ido ba.
"Daga baya, na fahimci abin da suke nufi, na fara kirga yatsun: daya, biyu, uku, hudu da sauransu."

- In ji tsohon makahon

Ya ce an fada masa ganinsa zai ci gaba da inganta a hankali, saboda ya shafe shekaru da dama ina makanta tun yana yaro.

Tsohon makahon ya ga fuskar diyarsu

Abin da ya fi ba shi mamaki shi ne ganin fuskar ’yarsa, domin bau taba ganinta da ido ba, shi ma kan shi bai san ya fuskar shi ta ke ba.

“Da muka koma gida, na kalle ta. Daga nan na yi amfani da kyamarar wayata wajen kallon fuskata.
Sai na fahimci cewa muna kama da juna. Matata ta sha gaya mani hakan, amma a wannan karon na gani da kaina.

Kara karanta wannan

Da gaske tsohon ministan Tinubu da ya rasa takara ya fara fada da APC?

Ganin ’yata shi ne abin da ya fi ba ni mamaki.
Na kuma yi mamakin ganin fuskar matata, amma farin cikin ganin ’yata ya fi yawa saboda yadda muka yi kama.

Har yanzu dai Abdullahi Abubakar yana amfani da jagora yayin da ganinsa nasa yake dawo wa.

makaho
Likita yana yi wa wani makaho aiki a asibitin Makkah a Kano Hoto: Makkah Specialist Eye Hospital Kano
Source: Facebook

An daure mataimakan 'yan Boko Haram

An ji labari cewa wani alkali ya yanke wa masu taimaka wa ’yan ta’adda hukuncin daurin rai da rai a kotun tarayya mai zama a Abuja.

Mataimakan kungiyar Boko Haram za su zauna a kukurku har ranar da ajali zai riske su saboda laifin da aka same su da aikatawa.

Alkali ya yanke wa Abba Mustapha da Bukar Ibrahim hukunci kuma an gurfanar da wasu masu irin laifinsu a wasu kotun na dabam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng