Da Gaske Tsohon Ministan Tinubu da Ya Rasa Takara Ya Fara Fada da APC?
- Tsohon Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ya musanta wani rahoto da ke cewa ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da jam'iyyar APC a fadin ƙasar
- Ofishin yada labaransa ya ce bidiyon da ake yadawa a kafafen sada zumunta tsoho ne, wanda aka cire wasu sassa aka gabatar da su ba tare adalci ba
- Adelabu ya jaddada cewa har yanzu yana biyayya ga APC da Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa yana neman adalci da gaskiya a harkokin cikin gida na APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya musanta wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da jam'iyyar APC a fadin ƙasar.
Ofishin yada labaransa ne ya fitar da sanarwa, inda ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da aka shirya domin bata masa suna da kuma haifar da rashin jituwa tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu da shugabannin APC.

Source: Facebook
Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook cewa ofishin ya bukaci jama'a da su yi watsi da rahoton, tare da neman waɗanda ke yaɗa shi su gabatar da sahihan hujjoji maimakon yada abin da ya kira bayanan da aka ƙirƙira.
Abin da Bayo Adelabu ya ce
A cewar sanarwar, Adelabu ya kasance mai biyayya ga APC da Shugaba Tinubu a tsawon tafiyarsa ta siyasa. Ya ce tsohon ministan bai taɓa yin watsi da jam'iyyar ba, kuma bai kira ga 'yan Najeriya su ƙi ta ba.
Sanarwar ta bayyana cewa Adelabu ya yi aiki a gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC a matsayin ministan makamashi, kafin ya bar mukamin bisa radin kansa domin neman takarar gwamnan jihar Oyo.
Ta kuma ce duk da korafe-korafen da ya yi kan tsarin zaɓen fitar da gwani na APC a Oyo, Adelabu ya sha bayyana cewa burinsa na siyasa ba abin da zai sa ya rabu da jam'iyyarsa ko Shugaba Tinubu ba.
Dalilin sukar zaɓen APC
Ofishin yada labaransa ya ce Adelabu ya nuna damuwa kan zargin fifita wani ɗan takara a zaɓen fitar da gwani na APC a jihar Oyo ba tare da bayyana sakamakon zaɓen a fili ba.
A cewar sanarwar, Adelabu ya yi tambaya kan yadda za a ayyana ɗan takara a matsayin wanda ya yi nasara ba tare da fitar da sakamakon zaɓen ba, sannan a kafa kwamitin sulhu domin sasanta waɗanda suka nuna rashin gamsuwa.
Sanarwar ta jaddada cewa neman adalci, gaskiya da bin ƙa'idojin dimokuraɗiyya a cikin jam'iyya ba yana nufin mutum ya yi watsi da ita ba.

Source: Facebook
Ofishin Adelabu ya bayyana cewa bidiyon da ake yadawa ya fito ne daga wata hira da ya yi a shekarar 2022, lokacin da yake takarar gwamnan jihar Oyo a ƙarƙashin jam'iyyar Accord.
Talaka ya ba 'yan APC kudi
A wani labarin, kun ji cewa wani direba a Ado-Ekiti, Adeleye Adeniyi, ya bayyana cewa ya ciwo bashin N3.5m domin tallafa wa Bola Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa Adeniyi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a cikin wani bidiyo da ya yaɗu ranar Juma'a.
Direban ya ce yana son tallafa wa 'yan siyasar ne saboda ya yi imanin cewa sun yi ayyukan alheri a mukaman da suka rike a baya.
Asali: Legit.ng


