"Ita Ta Nemeni Da Soyayya": Marubuci Makaho Yayi Tsokaci Kan Aurensa

"Ita Ta Nemeni Da Soyayya": Marubuci Makaho Yayi Tsokaci Kan Aurensa

  • Wani mai fama da lalurar gani amma mai ilimin gaske ya zanta da Legit.ng kan tarihin rayuwarsa
  • Ademola Adeleke wanda ya makance tun yana shekara 16 da haihuwa an angwance da wata kyakkyawar mata
  • Ademola Adeleke ya kamu da cutar Glaucoma wanda hakan yayi sanadiyar rasa idonsa

Oyo - Wani marubuci mai fama da jarabawar rashin gani ya bada labarin yadda ya hadu kyakkyawar matarsa da ta aureshi duk da halin da yake ciki.

A zantawarsa da Legit.ng, Ademola Adeleke ya yi bayanin yadda ya makance gaba daya tun yana dan shekara 16 sakamakon kamuwa da ciwon Glaucoma.

Adeleke, wanda mazaunin Ibadan a jihar Oyo na gab da fidda tsammani da zama wani a rayuwa sai ya samu gurbin karatu a jami'ar Najeriya dake Nsukka UNN.

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka Cikin Dare Kusa Da Dakin Hotel

Ya kammala karatunsa a ilmin aikin jarida (Mass Communication).

Demola Adeleke
"Ita Ta Nemeni Da Soyayya": Marubuci Makaho Yayi Tsokaci Kan Aurensa Hoto: Demola Adeleke
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A hirarmu da shi, ya bayyana cewa:

"Na kan shiga aji in saurari darasi. An koya min yadda zan yi amfani da Tafinta da komfuta.""
"Da rediyo nike daukan karatun, sai in saurara idan ina son nazari, lokacin jarabawa kuwa, ana karanto min tambayoyin sai in amsa cikin Komfuta."
Daga baya sai a fito da amsan da na rubuta a baiwa Lakcara don yin maki

Auren Adeleke

Adeleke ya samu auren wata kyakkyawar budurwa. Ya bayyanawa Legit cewa abin mamaki shine ita da kanta ta nemeshi da soyayya.

Yace:

"Abin al'ajabi game da rayuwata shine mata na da kanta tace tana sona. Na ji dadin haka."
"Tana taimaka min sosai, tana wasa da ni sosai, ina samun kwanciyan hankali da ita. Mutane da dama sun fada mata ta rabu da ni amma bata sauraresu ba. Gaskiya na yi dace."

Kara karanta wannan

Rikici: Tashin hankali yayin da kanin miji ya kwace wa dan uwansa mata mai 'ya'ya 7

Wani Matashi Ɗan Najeriya Na Shirin Wuf da Wata Baturiya Da Suka Hadu A TikTok

A wani labarin kuwa, Wani matashi mai suna Gideon Raphael da ke soyayya da wata baturiya ya yi nasarar haɗuwa da ita a zahiri.

Masoyan dai sun haɗu ne ta kafar sada zumunta, inda Raphael ɗin ya bayyana cewa sun sha soyayya ne na tsawon watanni uku kafin haɗuwar tasu.

Sannan Raphael ya saki wani bidiyo a TikTok da ke nuna yadda ya yi mata maraba a yayin da ta fito daga jirgin sama.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel