Kiwon Lafiya
Rahoto ya nuna cewa ma'aikata biyu sun mutu, wasu hudu sun kamu da zazzabin cizon sauro a filin jirgin Frankfurt bayan zargin sauro ya shigo Jamus a jirgin sama.
A labarin nan, za a ji cewa gwamantin jihar Kano ta bayyana damuwa game da rasuwar yara akalla 50 bayan bullar cutar mashako a karamar hukuma 1 tal.
A labarin nan za a ji cewa Majalisar dokokin jihar Kano ta bayyana damuwa bayan cutar mashako ta yi sanadin rasuwar yara akalla 50 a karamar hukumar 1.
Cutar ido mai saurin yaɗuwa da ake kira “Apollo” ta bulla a Jihar Bauchi, inda Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Abubakar Suleiman, ya ce ya kamu da ita.
Mutane huɗu yan gida ɗaya da karensu sun mutu bayan cin amala a Kogi. Gwamnati ta umarci Ma’aikatar Lafiya da ta binciki yiwuwar samun guba a abincin.
Daraktan UNIMEDTH, Farfesa Michael Gbala, ya yi gargadin cewa jabun magunguna na iya kashe mutane fiye da ’yan bindiga, tare da kira da a ƙara sa ido kan ingancinsu.
PHIMA ta rufe cibiyoyin lafiya masu zaman kansu 37 a Kano cikin watanni 18 saboda karya ƙa’idoji, yayin da sama da cibiyoyi 1,405 ke da rajista a jihar.
An tabbatar da cutar sake bullar Apollo a Potiskum, Yobe, yayin da mazauna suka koka kan saurin yaɗuwarta. Mahukunta sun ba da shawarwarin kariya.
Tarayyar Turai ta ware €2.3m ga Najeriya da wasu ƙasashe uku domin yaƙi da annobar kwalara, inda Najeriya za ta samu €1.5m daga cikin jimillar kudin.
Kiwon Lafiya
Samu kari