Kiristan Dan Siyasa Ya Tura Dubban Musulmi Makkah a Masa a Addu'a

Kiristan Dan Siyasa Ya Tura Dubban Musulmi Makkah a Masa a Addu'a

  • Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya ce ya shafe shekaru 25 yana aika mutane Makka domin yi masa addu’a
  • Akpabio ya bayyana cewa ba zai yi magana ta cin mutunci ga Musulunci ba, yana mai cewa ana fassara kalaman da yake yi a majalisa ba daidai ba
  • Ya kuma ce Musulunci ya haramta kashe kai da kisan mutane, yana mai jaddada cewa bai kamata a danganta ta’addanci da wani addini ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya ce ya shafe shekaru 25 yana aika mutane zuwa Makka domin yi masa addu’a da kuma yi wa ƙasar nan addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba.

Akpabio ya bayyana hakan ne a zaman majalisar ranar Alhamis, yayin da yake mayar da martani kan sukar da aka yi masa game da kalaman da ya yi lokacin muhawara kan kudirin dokar hana kashe kai ta shekarar 2026.

Kara karanta wannan

"Ba Musulmai ba ne," Shugaban majalisa ya gano wadanda suka hana zaman lafiya a Najeriya

Godswill Akpabio a majalisa
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

The Cable ta rahoto cewa yayin nazarin kudirin da Sanata Asuquo Ekpenyong, mai wakiltar Cross River ta Kudu, ya gabatar, Akpabio ya ce wasu matasa na tunanin kashe kansu saboda tunanin za su samu lada.

Kalaman nasa sun jawo suka daga wasu mutane da suka zarge shi da raina Musulunci.

Akpabio ya ce yana son Musulunci

Da yake mayar da martani kan sukar, Akpabio ya ce bai kamata a cire kalaman da ake yi yayin muhawarar majalisa daga mahallinsu ko a ɗauke su a matsayin hari kan wani addini ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Akpabio ya ce ya dade yana aika mutane Makka domin yi masa addu’a da kuma yi wa Najeriya addu’a.

Ya ce:

“Ina son addinin Musulunci. Ina aika mutane Makka domin yi min addu’a da kuma yi wa wannan ƙasa addu’a. Har zuwa jiya ina yin hakan, kuma na shafe shekaru 25 ina yi.”

Kara karanta wannan

2027: Dattijon Arewa da ya yi siyasa da Sardauna ya yi maganganu kan Tinubu

Akpabio ya ƙara da cewa wasu mutane na fitowa a shirye-shiryen talabijin suna fassara kalaman ‘yan majalisa ba daidai ba saboda siyasa.

Ya ce manufar ‘yan majalisa ita ce samar da dokoki masu amfani, don haka suna iya sabawa da juna a wasu batutuwa, amma kuma su goyi bayan juna a wasu lokuta.

Ya Musulmai 5,800 aikin Hajji

Shugaban majalisar ya ƙaryata zargin cewa zai yi magana ta cin mutunci ga Musulunci, inda ya yi nuni da dangantakarsa da Musulmai da kuma tallafin da ya bayar ga masu zuwa aikin ibada lokacin da yake gwamnan jihar Akwa Ibom.

Akpabio ya ce ya dauki nauyin Musulmai 5,800 zuwa ƙasa mai tsarki, sannan ya tura Kiristoci sama da 10,000 zuwa Roma da Urushalima.

Musulami na ibada a Makkah
Jama'a na dawafi a dakin Ka'aba. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Ya kuma bayyana cewa mataimakinsa na musamman kan harkokin tsaro, wanda ya kwashe shekaru 19 yana aiki da shi, Musulmi ne daga Azare da ke jihar Bauchi.

Ya ce fiye da kashi 65 cikin 100 na mutanen da ke aiki a ƙarƙashinsa Musulmai ne, yana mai cewa babu dalilin da zai sa ya raina addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Kisan Ayatollah Ali Khamenei ya damu Trump, ya nuna alamun nadama

Akpabio ya wanke Musulunci

A wani labarin, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Akpabio ya ce bai kamata a danganta ta’addanci da Musulunci ko Kiristanci ba.

Shugaban majalisar ya ce Musulunci ya haramta kashe kai da kashe wasu mutane, kuma addinin ba ya koyar da cewa wanda ya kashe kansa zai shiga Aljanna.

Sanata Akpabio ya kuma yi nuni da dokokin laifuffuka na Najeriya, waɗanda ya ce suna ɗaukar yunƙurin kashe kai a matsayin laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng