Kwankwaso Ya Sake Maganganu kan Atiku, Ya Tono Tsohon Tarihi

Kwankwaso Ya Sake Maganganu kan Atiku, Ya Tono Tsohon Tarihi

  • Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sa yake son Atiku Abubakar ya janyewa Peter Obi
  • Kwankwaso ya ce yana da doguwar alaƙar siyasa da Atiku, amma yana ganin lokaci ya yi da za a samar da sabon tsarin siyasa
  • Tsohon gwamnan Kano ya kuma bayyana cewa kiransa ba yana nufin yana adawa da Atiku ba, wanda suka daɗe suna aiki tare a harkokin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sa yake son tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya janyewa Peter Obi takara a zaɓen 2027.

Da aka tambaye shi ko yana nan kan bakarsa ta cewa Atiku ya kamata ya janye takararsa a wannan karon, Kwankwaso ya amsa da cewa, “Eh.”

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya yi hasashen nasarar Bola Tinubu a Najeria

Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar
Rabiu Kwankwaso a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Atiku Abubakar|Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels Television ya yi da shi a shirin Politics Today ranar Alhamis, inda ya yi bayani kan doguwar alaƙar siyasarsa da Atiku da kuma dalilin haɗin gwiwarsa da Obi.

Dalilin son Atiku ya janye

Kwankwaso ya ce bai yi wannan kira ne saboda yana ƙiyayya da Atiku ba, yana mai bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasar a matsayin wanda suka daɗe suna aiki tare.

Ya ce:

“Mai girma mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, mutum ne da na san shi sosai. Mun yi abubuwa da dama tare a baya. A gaskiya, fiye da kowa da ke tare da shi a yanzu.”

Kwankwaso ya bayyana cewa yana ganin ya kamata a yi la’akari da tarihin alaƙarsu da kuma damar samar da sabon tsarin siyasa a ƙasar nan.

Kwankwaso ba ya adawa da Atiku

Da yake taƙaita matsayinsa, Kwankwaso ya jaddada cewa bai kamata a fassara kiransa na neman Atiku ya janye takara a matsayin ƙiyayya ko adawa da shi ba.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike ya sake fallasa abin da wasu daga cikin gwamnoni suka yi masa

Ya ce sun yi aiki tare a lokuta da dama, amma akwai lokacin da ya kamata a sauya tsari domin samar da wata sabuwar hanya a siyasa.

Kwankwaso ya ce:

“Abin da nake ƙoƙarin faɗa shi ne, ba mu adawa da shi. Mun yi aiki tare da shi, don haka komai yana da lokacinsa.”
Rabiu Musa Kwankwaso
Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Alakar Kwankwaso da Atiku

Kwankwaso ya ce alaƙar siyasarsa da Atiku ta samo asali ne tun shekarar 1993, lokacin da suke cikin tafiyar siyasa ƙarƙashin jagorancin marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua.

Ya bayyana cewa a wancan lokaci, sun goyi bayan Atiku domin ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP.

Kwankwaso ya ce:

“A shekarar 1993, yana cikin ƙungiyarmu ƙarƙashin jagorancin Janar Shehu Yar’Adua, kuma shi ne zaɓinmu na ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP.”

Ya ƙara da cewa sun yi duk mai yiwuwa domin Atiku ya samu tikitin takarar, amma hakan bai yiwu ba. Daga nan suka yi ƙoƙarin ganin an ba shi tikitin mataimakin shugaban ƙasa.

Duk da cewa ƙoƙarin bai yi nasara ba, Kwankwaso ya ce alaƙarsu ta ci gaba har zuwa shekarar 1999, lokacin da Olusegun Obasanjo ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

2027: Dattijon Arewa da ya yi siyasa da Sardauna ya yi maganganu kan Tinubu

Ya tuna cewa a lokacin yana gwamnan Kano da aka zaɓa, yayin da Atiku ya zama mataimakin Obasanjo.

Atiku ya kafa 'Ask AA'

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da wani dandali mai suna Ask AA.

An tsara ƙaddamar da dandalin ne da ƙarfe 8:30 na dare ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026, domin jama’a su tambayi Atiku game da tarihin aikinsa na gwamnati da manufofinsa.

Dandalin zai ba ’yan Najeriya damar tattaunawa da Atiku kan tattalin arziki, tsaro, fasaha, samar da ayyukan yi da kuma tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng