An Kama Masu Taimaka wa Boko Haram, Kotu Ta Yanke Masu Tsattsauran Hukunci

An Kama Masu Taimaka wa Boko Haram, Kotu Ta Yanke Masu Tsattsauran Hukunci

  • Wata Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta yanke wa Abba Mustapha da Bukar Ibrahim hukuncin dauri
  • Za su zauna a gidan gyaran hali har su bar duniya saboda an same su da laifin taimaka wa ’yan Boko Haram
  • Hukuncin ya zo ne da gwamnatin tarayya ke ci gaba da gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a ta’addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Wasu masoya kuma masu taimaka wa ‘yan Boko Haram da bayanai sun gamu da hukuncin da ya dace da irin laifinsu.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu mutane biyu hukuncin daurin rai da rai bayan samun su da assha.

Sojoji
Sojojin da suke gwabzwa da Boko Haram a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An daure masu taimakon 'yan Boko Haram

Daily Trust ta ce an kama su da laifin taimaka wa kungiyar ’yan ta’addan Boko Haram da suka shafe shekaru suna ta’adi.

Kara karanta wannan

Yadda tawagar ofishin Ribadu suka ceto mata, miji da jaririyarsu da aka sace

Wadanda aka yanke wa hukuncin su ne Abba Mustapha da Bukar Ibrahim, wadanda suka fito daga Borno a Arewa maso gabas.

Alkali Salim Ibrahim ne ya yanke hukuncin bayan mutanen biyu sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi a kotun na Abuja.

An zarge su da taimaka wa kungiyar da kuma boye bayanan da suka shafi ayyukanta.

Daurin rai da rai da daurin shekaru 20

Kotun ta yanke wa kowannensu hukuncin daurin rai da rai kan tuhuma ta farko saboda sun ba ‘yan Boko Haram agaji.

Haka kuma, ta yanke musu hukuncin daurin shekaru 20 kan tuhuma ta biyu a cewar rahoton gidan rediyon Najeriya na FRCN.

An yanke hukuncin ne a yayin da gwamnatin tarayya ta sake fara shari’ar wasu mutane da ake zargi da hannu a ta’ddanci.

Ana tuhumarsu da ayyukan ta’addanci da taimaka wa ’yan ta’addan da aka yi shekaru kusan 20 ana fama da su a yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Kaico: Mutane da dama sun mutu yayin da suka je ɗibar ganima jikin wata tankar fetur

Shari'a da masu taimaka wa Boko Haram

An ji cewa ana gudanar da shari’o’in ne a dakunan kotu daban-daban a birnin tarayya Abuja.

Daga cikin alkalan da ke jagorantar shari’o’in akwai Salim Ibrahim, James Omotosho, Binta Nyako, Emeka Nwite da Obiora Egwuatu.

Sauran alkalan su ne Hauwa Yilwa, Joyce Abdulmalik da Mai shari’a Peter Lifu.

An sanya sunayen mutane 34 da za su gurfana a gaban Alkali Salim Ibrahim, yayin da aka sanya wasu 25 a gaban Alkali Peter Lifu.

Gwamnati ta dage wajen shari'a da 'yan ta'adda

A watan Yuni, gwamnatin tarayya ta gurfanar da sama da mutane 600 da ake zargin suna da alaka da kungiyoyin ta’addanci a Najeriya.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya yi magana bayan nasarar da suka samu a kotun.

Fagbemi SAN ya ce matakin na nuna cewa gwamnati ba ta daukar batun ta’addanci da wasa.

Boko Haram a Najeriya Hoto: Getty Images
'Yan Boko Haram a garin Baga, jihar Borno Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kama 'yan Najeriya a kasar Amurka

Ana da rahoto cewa Hukumomin Amurka sun yi ram da wasu mutanen Najeriya da ake zargi da aikata laifuffuka a kasar wajen.

Kara karanta wannan

Kasar Amurka ta saki sunayen ‘yan Najeriya 24 da aka kama da kuma laifuffukansu

An cafke wadannan bayin Allah da zargin damfara, wanke kudin haram da mu’amala da kwayoyi, wadanda duk saba wa dokoki.

Akwai wadanda ake tuhuma da amfani da takardun bogi, sojan gona da cin zarafin yara a Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng