"Zan So Ka Dawo APC," Hadimin Tinubu Ya Aika Sako ga Dan Takarar Shugaban Kasa a 2027

"Zan So Ka Dawo APC," Hadimin Tinubu Ya Aika Sako ga Dan Takarar Shugaban Kasa a 2027

  • Daniel Bwala ya yi fatan Gwamna Seyi Makinde zai shiga APC ya goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027
  • Hadimin shugaban kasar ya ce Makinde zai ci amanar Kudancin Najeriya idan ya mara wa Atiku Abubakar baya
  • Bwala ya ce ba ya ganin Atiku ko Peter Obi na jam'iyyar NDC zai janye takararsa domin ya marawa ɗayan baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Daniel Bwala, ya bayyana fatan cewa Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, zai shiga jam’iyyar APCtare da goyon bayan tazarcen Tinubu a 2027.

Bwala ya ce ya fi son Makinde ya haɗa kai da su maimakon tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.

Bwala da Tinubu.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Daniel Bwala tare da Bola Tinubu Hoto: Daniel Bwala
Source: Twitter

Hadimin shugaban kasa ya yi wannan furuci ne yayin da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Makinde ya shirya marawa Atiku baya a zaɓen 2027? An samu bayanai

Hadimin Tinubu ya gargadi Makinde

Ya gargaɗi gwamnan cewa zai ci amanar Kudancin Najeriya idan ya goyi bayan Atiku a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa ya kamata kujerar shugaban ƙasa ta ci gaba da kasancewa a Kudu har tsawon shekaru takwas.

Bwala ya ce yana da yakinin cewa Makinde zai iya haɗa kai da Tinubu a nan gaba, amma yana da damuwa kan alaƙar siyasar da ake cewa gwamnan na kullawa da Atiku.

“Ina da yakinin cewa nan gaba Seyi Makinde zai shigo jam’iyyar Asiwaju. Amma mu ɗauka bai yi hakan ba. Mutanen da yake jagoranta ba wawaye ba ne, ya kamata mulki ya ci gaba da kasancewa a Kudu har tsawon shekaru takwas,” in ji shi.

Bwala ya ce goyon bayan da Makinde zai bai wa Atiku zai zama cin amanar al’ummar Kudu, saboda muradun yankin na ganin an ci gaba da riƙe shugabancin ƙasa bayan wa’adin farko na Tinubu.

Kara karanta wannan

'Matsalar da Atiku zai ci karo da ita a yankinsa na Arewa maso Gabas'

Makinde zai iya hada kai da Atiku?

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa yake ganin Makinde zai iya goyon bayan Atiku, hadimin shugaban ƙasar ya yi zargin cewa tuni an cimma matsaya kan wannan yarjejeniya, yana mai cewa abubuwan da za su faru za su tabbatar da maganarsa.

“An riga an cimma matsaya kan hakan a ƙa’ida, kuma za ku ga abin da nake faɗa,” in ji Bwala.

Ya kuma nuna shakku kan damar Makinde idan ya yanke shawarar tsayawa takarar shugaban ƙasa shi kaɗai, yana mai cewa zai sha wahala wajen kayar da Tinubu a Jihar Oyo.

Bwala ya gargaɗi gwamnan cewa irin wannan mataki na iya kawo ƙarshen makomarsa ta siyasa.

Gwamna Makinde.
Dan takarar shugaban kasa na APM, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Bwala ya sake tabo Atiku da Peter Obi

Hadimin shugaban ƙasar ya kuma yi watsi da yiwuwar Atiku ko Peter Obi ya janye takararsa domin ya mara wa ɗayan baya gabanin zaɓen, yana mai cewa dukkansu suna da alƙawura masu ƙarfi ga magoya bayansu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi abin da zai yi wa Tinubu idan ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2027

Bwala ya ce magoya bayan Obi, musamman yan Obidient Movement, suna sa ran zai tsaya takarar shugaban ƙasa. Ya ce janyewarsa domin goyon bayan wani ɗan takara zai zama cin amanar amincewar da suka yi masa.

Bwala ya hango faduwa a jihohi 2

Kun ji cewa mai ba shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan sadarwa da dabaru, Daniel Bwala, ya yi hasashen jihohin da APC za ta iya shan kaye a zaben 2027.

Bwala ya ce APC za ta lashe jihohi uku a yankin Kudu maso Gabas a zaɓen 2027, sannan ya amince cewa Peter Obi na iya ci gaba da samun galab a Abia da Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262