Nafiu Bala Zai Fara Yakin Neman Zabe, Yana Tunanin Ya Tafi da Atiku Abubakar a ADC

Nafiu Bala Zai Fara Yakin Neman Zabe, Yana Tunanin Ya Tafi da Atiku Abubakar a ADC

  • Nafiu Bala ya ce zai fara yakin neman zaben shugaban kasa a mako mai zuwa, yana takamar ’yan Najeriya na goyon bayansa
  • Ya nuna yana tunanin nada Atiku Abubakar a matsayin Darakta-janar na kwamitin yakin neman zabensu idan ya yi rajista da ADC
  • Wannan na zuwa ne bayan kotu ta soke shugabancin ADC karkashin David Mark aka kuma kawo wa takarar Atiku babban cikas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ADC na shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala, ya bayyana cewa zai fara harkar kamfe.

A makon da za a shiga Nafiu Bala zai kama yakin neman zaben shugaban kasa, zai shiga tallata ‘dan takaran da yake tare da shi a ADC.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar yana yakin neman zabe a jam'iyyar ADC a Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Bangaren Nafiu Bala zai shiga kamfe

The Cable ta ce Nafiu Bala ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi biyo bayan nasarar da yake ganin ya yi a kan tsagin David Mark.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya faɗi jihohi 2 da APC za ta iya shan laye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Matashin ya ce ba ya tsammanin za a kai masa hari ko a ci masa zarafi saboda fara yakin neman zabensa, ya ce ’yan Najeriya suna kaunarsa.

Ya ce:

“Za mu fara yakin neman zaben shugaban kasa a mako mai zuwa. Babu wanda zai kai mana hari saboda ’yan Najeriya suna kaunarmu.”

Nafiu Bala zai iya ba Atiku Abubakar DG

Haka kuma, Nafiu Bala ya bayyana cewa yana tunanin bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, mukamin darakta-janar (DG)

Tsohon mataimakin shugaban kasar zai iya zama shugaban kwamitin yakin neman zabensa, amma da sharadin Atiku ya shigo cikin ADC da kyau.

A yanzu duk abin da ake yi, tsohon mataimakin shugaban na ADC yana ganin cewa su Atiku da mutanen bangarensa ba ‘yan jam’iyyarsu ba ne.

Chris Uba ne 'dan takaransu Nafiu a ADC

A wajen su Nafiu Bala, Farfesa Chris Uba da Dr Shamsuddeen Modibbo Barkindo ne suke yi wa jam’iyyar adawa ta ADC takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Dattawa sun shiga magana, ana ta tir da sakin auren gwamna Abba a jihar Kano

Chris Uba gawurtaccen ‘dan siyasa ne daga Anambra wanda aka dama shi da kyau a kasar nan musamman lokacin mulkin Olusegun Obasanjo.

Duk da Nafiu ya ce ba za su ba tsoho takarar shugaban kasa a 2027 ba, Sun ta rahoto cewa Uba da tsaginsa ya ba tikiti ya kai shekara 71 a duniya.

Rikicin shugabancin jam'iyyar ADC

Shirin shi fara kame na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin shugabanci a jam’iyyar ADC, ana ganin an soke takarar Alhaji Atiku Abubakar.

A Satumban 2025, Nafiu ya shigar da kara a a kotu a Abuja, inda ya nemi hana su David Mark da gabatar da kansu a matsayin shugabannin ADC.

Wadannan shugabannin ne suka kori Nafiu da wasu mambobin jam’iyyar kuma su ne suka tsaida Atiku Abubakar a matsayin ‘dan takaransu a 2027.

Nafiu Bala
Tsohon mataimakin shugaban ADC na kasa, Nafiu Bala Hoto: Hon. Nafiu Bala
Source: Facebook

Alƙali ya jiƙa wa Atiku aiki a ADC

A ranar 5 ga Nuwamban 2026, aka ji labari babbar kotun tarayya ta soke kwamitin rikon kwarya da Mark ke jagoranta, ya kuma rusa duk matakansa.

Kara karanta wannan

Matsalar aure: Abba ya tashi tawaga zuwa gidan Kwankwaso domin a sasanta

Peter Lifu ya yanke hukuncin cewa kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin David Mark, wanda ya shirya zaɓen fitar da gwani bai da hurumi.

F ta goyi bayan Nafiu Bala da ta ce NWC da ya fito da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar ADC, haramtaccen kwamiti ne a tsarin dokar ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng