Hare Hare kan Obi, Kwankwaso Ya Fara Tono Boyayyun Abubuwa, NDC Ta Yi Gargadi
- Jam’iyyar NDC ta sha alwashin ci gaba da fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 duk da zargin fuskantar barazana da hare-hare
- Shugaban jam’iyyar, Sanata Moses Cleopas, ya zargi gwamnatin da ke mulki da ƙoƙarin raunana ’yan adawa ta hanyar tsoratarwa
- NDC ta bayyana cewa ba za ta tilasta wa Peter Obi ko sauran ’yan takararta janyewa daga zaɓen ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa ba za ta janye daga tseren zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
Jam'iyyar ta ce akwai zargin fuskantar barazana, cin zarafi da hare-hare kan mambobinta da ’yan takararta domin tsoratar da su.

Source: Facebook
NDC na zargin ana so hana Obi takara
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Moses Cleopas, ne ya bayyana matsayar a ranar Laraba yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, cewar PM News.
Ya zargi wasu masu hannu da shuni a gwamnati da ƙoƙarin amfani da tashin hankali da tsoratarwa domin raunana jam’iyyar da hana ta gudanar da harkokin siyasa gabanin babban zaɓen 2027.
Ya yi tambaya kan dalilin da ya sa NDC da Obi suke fuskantar hare-hare akai-akai, alhali sauran jam’iyyun siyasa ma suna shirin shiga zaɓen da ke tafe.
Shugaban jam’iyyar ya ce:
“Ba ’yan takararmu kaɗai ne ke neman muƙaman zaɓe a wannan ƙasa ba. Musamman ma, Mista Peter Gregory Obi ba shi ne kaɗai ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen da ke tafe ba. Don haka, tambayar ita ce, me ya sa NDC da ɗan takararta suke fuskantar hare-hare da cin zarafi a koda yaushe?
“Amsar da za a iya bayarwa ita ce, gwamnatin da ke kan mulki tana tsoron ɗan takararmu na shugaban ƙasa, Peter Obi, da sauran ’yan takarar NDC.”

Source: Instagram
Abin da NDC ta gano kan lamarin

Kara karanta wannan
Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur
Cleopas ya bayyana cewa abubuwan da ke faruwa wata dabara ce da aka shirya domin rufe bakin ’yan adawa da kuma kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama a Najeriya.
Ya ce ba za su amince da duk wani yunƙuri na kai hari ga Peter Obi ko sauran ’yan takararsu a wasu sassan ƙasar ba, yana mai cewa hakan wata alama ce ta shirin da aka tsara domin murƙushe jam’iyyar, cewar Punch.
NDC ta nemi taimakon Amurka
An ji cewa jam’iyyar NDC ta nemi Amurka da Tarayyar Turai su sa baki kan zargin kai hare-hare da tsoratar da ’yan adawa a Najeriya.
NDC na zargin jam'iyya mai mulki ta APC da neman hana jam'iyyun adawa sakat musamman da ake tunkarar zaben shekarar 2027.
Sai dai NDC ta ce ba za ta tsorata ko janye daga zaɓen 2027 ba, tana mai cewa dole ne a ƙirga tare da sanar da ƙuri’un da ta samu.
Asali: Legit.ng
