Kisan Ayatollah Ali Khamenei Ya Damu Trump, Ya Nuna Alamun Nadama

Kisan Ayatollah Ali Khamenei Ya Damu Trump, Ya Nuna Alamun Nadama

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince cewa kasar tasa na iya wuce gona da iri wajen kai hari kan shugabannin Iran, lamarin da ya ce ya kawo cikas
  • Trump ya yi ikirarin cewa sojojin Iran sun rasa jiragen ruwan yaki 159, yayin da ya jaddada cewa ba za a bari kasar ta mallaki makaman nukiliya ba
  • Hakan na zuwa ne yayin da Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake zargi da daukar yara aikin soja, matakin da ka iya shafar tallafin tsaro da sayar da makamai ga kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa kasarsa na iya wuce gona da iri wajen kai hari kan shugabannin Iran.

Ya yi magana yana mai cewa kashe manyan jami’an kasar ya kara wahalar gano mutanen da Washington za ta iya tattaunawa da su domin kawo karshen rikicin.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya zafafa da ya kwatanta Tinubu da dakikin dalibi

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Middle East Eye ta wallafa cewa Trump ya fadi haka ne ranar Litinin yayin wani gangamin siyasa a Youngstown, da ke jihar Ohio, inda ya yi magana kan kalubalen da Amurka ke fuskanta wajen neman mafita ta diflomasiyya ga rikicin da take yi da Iran.

Ya ce:

“Mai yiwuwa mun wuce gona da iri wajen kai hari kan shugabannin, domin yanzu ba mu san wadanda muke mu’amala da su ba.”

Trump ya kara da cewa babu wanda yake son zama shugaban Iran, yana mai ikirarin cewa wadanda za su iya rike mukamin ba sa son karbarsa.

Trump ya yi maganar nukiliya

A yayin jawabin nasa, Trump ya sake jaddada cewa Amurka ba za ta bari Iran ta mallaki makaman nukiliya ba, yana mai bayyana kasar a matsayin babbar mai daukar nauyin ayyukan ta’addanci a duniya.

Duk da amincewarsa cewa kai hare-hare kan shugabannin Iran ya kawo matsaloli wajen tattaunawa, Trump ya ci gaba da ikirarin cewa hare-haren sojin Amurka sun raunana rundunonin sojin saman da na ruwan Iran sosai.

Kara karanta wannan

Jarumin Kannywood Adam Zango ba lafiya, mutane na ta masa addu'o'i

Ya yi ikirarin cewa Iran ta rasa jiragen ruwan yaki guda 159, yana mai cewa dukkansu suna karkashin teku.

Sai dai bayanan da aka bayar a jawabin ba su kunshi karin bayani mai zaman kansa da zai tabbatar da wannan ikirari ba.

Trump ya gaza shawo kan Iran

Jerussalem Post ta wallafa cewa maganganun Trump sun yi kama da damuwar da Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana a wata hira da ya yi.

Vance ya ce Washington ba ta da cikakken tabbaci kan yadda ake yanke shawara a cikin shugabancin Iran.

Ya kuma jaddada cewa duk wata yarjejeniya da za ta kawo karshen rikicin za ta bukaci Iran ta dauki matakai masu ma’ana wajen rage karfin tace sinadaran nukiliyarta.

Ali Khamenei na Iran
Ayatollah Ali Khamenei da aka kashe a Iran. Hoto: Getty Images
Source: AFP

Wannan na nuna cewa gano mutanen da za su iya shiga tattaunawa da kuma cimma yarjejeniya na daga cikin kalubalen da Amurka ke fuskanta yayin neman mafita ga rikicin.

Amurka ta gargadi Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake zargi da daukar yara aikin soja, bisa tanadin dokar kasar.

Kara karanta wannan

Bayan rage farashi, Gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan yiwuwar dawo da tallafin fetur kafin 2027

Rahoton Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka kan safarar mutane na shekarar 2026 ya danganta matakin da ci gaba da daukar yara da amfani da su.

Rahoton, wanda aka wallafa ranar 11 ga Oktoba, ya kunshi nazarin yadda Najeriya ke yaki da safarar mutane daga ranar 1 ga Afrilu, 2025 zuwa 31 ga Maris, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng