Sabbin masarautu: Al'ummar karamar hukumar Wudil sun bijire wa Ganduje

Sabbin masarautu: Al'ummar karamar hukumar Wudil sun bijire wa Ganduje

Biyo bayan nadin sabbin sarakunan yanka guda hudu da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi a ranar Asabar, wasu kungiyoyin al'umma a karamar hukumar Wudil sun bijire wa masarautar Gaya da suka fada a karkashinta, tare da bayyana mubaya'ar su ga masarautar Kano.

Da yake magana da manema labarai jim kadan bayan kammala taron kungiyoyin al'umma a karamar hukumar Wudil, Malam Muhammad Idris, shugaban gamayyar kungiyoyin tare da sakatarensa, Dakta Baba Sani Wudil, sun bayyana cewar ba a tuntubi al'ummar karamar hukumar Wudil ba kafin a kirkiri sabbin masarautun, a saboda haka an saba wa tsohon tarihin da yankin keda shi.

"Ba mu nemi a kirkiri sabuwar masarauta ba, kuma da gwamnati tayi niyyar yin hakan ba ta tuntubi jama'ar karamar hukumar Wudil ba. Mun tabbatar da cewar sabuwar dokar masarautun da gwamnati ta kirkira za ta lalata tsohon tarihin da Wudil keda shi.

Sabbin masarautu: Al'ummar karamar hukumar Wudil sun bijire wa Ganduje
Ganduje da Sarki Sanusi II
Asali: Facebook

"Mu na da dogon tarihi a karkashin tsohuwar masarautar Kano a matsayin mu na 'Jobawa', kuma mu na son gwamna Ganduje ya san da hakan.

"Da wannan muke son sanar da cewar dukkan masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Wudil su na biyayya ne ga masarautar Kano ba Gaya ba," a cewar sa.

DUBA WANNAN: Sabbin Sarakuna: Mun yiwa dokar garambawul, babu mai iya canja ta - Ganduje

Ya kara da cewa al'ummar karamar hukumar Wudi zasu mika koken su ga dukkan hukumomin da abin ya shafa domin a duba bukatar su.

A cewar sa, masu da ruwa da tsaki a Wudil zasu bi duk hanyoyin da suka dace da dokokin Najeriya domin ganin cewarv sun cigaba da zama a karkashin tsohuwar masarautar Kano ba sabuwar masarautar Gaya da gwamna Ganduje ya kirkira ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel