Latest
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya gaya wa Buhari shirinsa na barin APC kuma sai da ya amince sannan ya koma SDP.
Rundunar 'yan sandan kasar nan ta yi nasarar hallaka matashin dan ta'adda, Dogo Saleh, wanda aka hakikance ya jawo asarar rayukan jama'a da dama bayan garkuwa da su.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron da ke cikin ayarin Gwamna Babagana Umaru Zulum sun fatattaki ƴan Boko Haram da suka tare matafiya a Borno.
Rundunar tsaro ta dakile harin ramuwar gayya na ‘yan bindiga a Mada, karamar hukumar Gusau, jihar Zamfara inda ta yi nasarar hallaka hatsabibin dan ta'adda.
ICPC ta gurfanar da jami’in NIS, Abubakar Aseku, bisa zargin karɓar N17.6m daga ma’aikatu uku. Kotu ta ba shi beli, an daga shari’a zuwa Afrilu 29.
Shugaban kungiyar Arewa Summit International, Bashir Lamido ya yi magana kan yiwuwar faduwar Bola Tinubu a 2027 inda ya ce zai yi wahala shugaban kasa ya sha kasa.
Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta yi fatali da ƙarar da wata kungiya fa shigar a madadin karuwai, inda ta ƙalubalanci matakin da ministan Abuja ke ɗauka.
Jam'iyyar NNPP mai adawa ta harzuka kan kalaman da Nasir El-Rufai ya yi na cewa gwamnatin tarayya na da hannu a cikin rikicin da ya addabe ta. Ta ba shi wa'adi.
Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 3 a Kaduna, sun kwato makamai, alburusai, wayar salula, magunguna da kayan abinci yayin farmaki kan ‘yan ta’addan.
Masu zafi
Samu kari