2027: An Jero Mutum 2 a Arewa da idan Suna tare da Tinubu ba Zai Fadi Zabe ba
- Shugaban wata kungiya a Arewa, Dr. Bashir Lamido ya ce babu yiwuwar Bola Tinubu zai fadi a 2027 saboda yana da manyan ’yan siyasa
- Lamido ya bayyana cewa hadin kai tsakanin Abdulaziz Yari, Abdullahi Ganduje, James Ibori da Sanata Orji Kalu zai lalata shirin ‘yan adawa
- Ya soki rashin daidaito tsakanin jam’iyyun adawa, ya ce babu tabbacin cewa za su iya cimma matsaya daya kafin 2027 da za a yi babban zabe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban Arewa Summit International, Dr. Bashir Lamido ya yi magana kan yiwuwar faduwar Bola Tinubu a zaben 2027.
Lamido ya ce babu yiwuwar shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu zai sha kaye a 2027 idan na jikinsa na tare da shi.

Asali: Facebook
2027: Tasirin da ake ganin Ganduje zai yi

Kara karanta wannan
Bayan rasa El-Rufai, gwamnatin Tinubu ta fadi dan takarar shugaban kasa da zai dawo APC
Lamido ya fadi haka ne yayin da yake amsa tambayoyi daga 'yan jarida a Abuja, cewar rahoton The Sun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamido ya ambaci Abdulaziz Yari, Sanata Orji Kalu, Abdullahi Ganduje da James Ibori da cewa za su yi tasiri a nasarar Tinubu.
Ya ce kasancewar manyan 'yan siyasa masu karfi a bayan Tinubu, hakan zai sa faduwar zabensa a 2027 ya zama da kamar wuya.
Ya kara da cewa hadin gwiwar wadannan 'yan siyasa tare da Tinubu zai raunana adawa kuma ya tabbatar da nasarar APC a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Lamido ya kalubalanci ikon hadakar jam’iyyun adawa na kafa dunkulalliyar kawance kafin 2027 tare da cimma matsaya daya tsakanin su.
A cewarsa:
“Idan ana magana kan karfin adawa su kwace mulki, ya kamata a tambaya ko za su iya daidaita tsakaninsu?”
“Wane ne zai tsaya takara? Atiku Abubakar ko Peter Obi? El-Rufai ko Osinbajo? Amaechi ko Saraki?”

Asali: Facebook
Lamido ya yi hasashen rikici a jam'iyyun adawa
Lamido ya ce PDP da LP na cikin rikice-rikicen cikin gida sosai, sannan jam'iyyar SDP kuwa ba ta da tabbacin jagorantar kawance.
Ya kara da cewa dukkansu suna da muradin takarar shugaban kasa amma ba su da niyyar janyewa don wani.
Ya ce:
“Tinubu mai hankali ne kuma mai dabara, wasu suna tunanin Yari, Kalu da Ibori za su koma adawa.”
“Na ji cewa El-Rufai ya yi kokarin kawo sabani tsakanin Tinubu da Ganduje ta hanyar tura shi Saudi a matsayin jakada.”
“Yanzu Tinubu ya sulhunta da su kuma suna cikin aminansa na kut-da-kut, sun riga sun amince da goya masa baya.”
“Wadannan mutum hudu dukkansu na da kwarewar shugabanci amma sun rungumi Tinubu, tare da su, ba zai fadi ba."
Lamido ya ce Yari na aiki da matasa a Arewa, Kalu na yi a yankin Kudu har ma yana fadadawa zuwa Arewa, sauran su ma haka suke.
Ana hasashen Peter Obi bi Bola Tinubu
Kun ji cewa Hadimin shugaba kasa, Daniel Bwala ya ce dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi zai bar jam'iyyarsa ya koma APC kafin zaben 2027.
Bwala ya ce sauya shekar Valentine Ozigbo alamu ne na faduwar jam’iyyar LP a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng