Ayarin Gwamna Zulum ya gwabza da ƴan Boko Haram, rayuka da dama sun salwanta

Ayarin Gwamna Zulum ya gwabza da ƴan Boko Haram, rayuka da dama sun salwanta

  • Dakarun sojoji da sauran jami'ann tsaro da ke tawagar gwamnan Borno sun fatattaki ƴan ta'addan Boko Haram a titin Buni Gari-Buni Yadi
  • An ruwaito cewa jami'an tsaron sun kashe ƴan ta'addan da ba a tantance adadinsu ba a musayar wuta, kuma sun kwato fasinjoji bakwai
  • Ɗaya daga cikin fasinjojin da jami'an tsaron suka ceto ya ce ƴan ta'addan sun tare su kwatsam sai ga ayarin motocin mai girma gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Jami’an tsaron ayarin Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno sun dakile harin da ‘yan Boko Haram suka kai kusa da garin Gujba.

Wannan lamari ya faru ne lokacin da tawagar gwamnan ke dawowa daga garin Biu bayan kaddamar da wasu ayyuka a ƙananan hukumomin Biu da Hawul.

Gwamna Zulum.
Ayarin gwamnan jihar Borno sun ci karo da ƴan Boko Haram Hoto: @ProfZulum
Asali: Twitter

Masani kuma mai sharhi kan al'amuran tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ya tabbatar da hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

"Babu wanda zai dawwama a mulki," Gwamna ya ji haushin abin da aka masa a Majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa sojojin sun daƙile harin da ƴan ta'addan suka yu yunƙurin kai wa ayarin Zulum, sannan sun kashe da dama daga cikinsu.

Ayarin Zulum sun fatattaki ƴan Boko Haram

Mayakan Boko Haram na yunkurin sace fasinjoji a kan titin, kwatsam sai ga ayarin Gwamna Zulum, daga suka tarbe su aka fara azababben musayar wuta.

"Nan take sojoji da sauran jami'an tsaron suka far wa ƴan Boko Haram, suka gwabza kazamin faɗa wanda daga bisani ƴan ta'addan suka fara yunkurin guduwa.
"Dakarun tsaron suna ci gaba da bin ƴan ta'addan da harbi, suka kashe da dama daga cikinsu, sannan suka kwato makamai da babu.
"Babu wanda ya samu rauni daga cikin mutanen ayarin motocin gwamna kuma sojojin sun yi nasarar ceto fasinjoji bakwai,"

0 in ji Makama.

An ruwaito cewa Gwamna Zulum ba ya cikin ayarin a lokacin da lamarin ya faru, ya bi jirgi mai saukar angulu zuwa Maiduguri bayan kammala taron.

Kara karanta wannan

Zamfara: An hallaka hatsabibin ɗan ta'adda da aka daɗe ana nema ruwa a jallo

Yadda ƴan ta'addan suka tare fasinjoji

Daya daga cikin fasinjojin da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda ‘yan ta’addan suka umarci fasinjojin da su kwanta a kasa, amma da suka ga tawagar gwamna, sai suka gudu.

“Sun tarwatsa mu, sun kwace mana makullin mota. Daya daga cikinsu ya saita bindiga yana shirin harbi na, amma da suka ga tawagar gwamna, sai suka tsere da gudu,”

- in ji shi.

Gwamna Zulum.
Ayarin gwamnan Borno ya daƙiƙe harin yan ta'adda Hoto: Prof. Babagana Zulum
Asali: UGC

Ƴan Boko Haram sun matsa da hare-hare

Fasinjojin sun koka kan yadda ‘yan Boko Haram ke yawan tare hanya da kai hare-hare a yankin Gujba.

Kwanaki uku da suka gabata, maharan sun kai hari a garin Gujba da ke kan titin, suka kashe wani mai gadi mai suna Modu Bulama. Sun kuma banka wa shaguna da gidaje wuta.

A cewar fasinjojin da aka ceto, ya kamata jami'an tsaro su kara zage dantse domin tabbatar da tsaro a wannan hanya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Kaduna, an samu asarar rayuka

Ƴan ISWAP sun farmaki makiyaya

A wani rahoton, kun ji cewa miyagun 'yan ta'addan ISWAP sun kai hari kan sansanin Fulani makiyaya a jihar Borno kwanan nan.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun shiga yankin ne a kafa, sannan suka bude wuta kan kan mai uwa da wabi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng