Rashin Tsaro Ya Jefa Majalisa a Rudani, An Sake Gayyatar Ribadu da Hafsun Sojoji

Rashin Tsaro Ya Jefa Majalisa a Rudani, An Sake Gayyatar Ribadu da Hafsun Sojoji

  • Majalisar Dattawa ta bayyana damuwarta kan karuwar matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na Najeriya
  • A zaman da majalisar ta yi a ranar Laraba, ta sake gayyatar shugabannin tsaro su bayyana a gabanta mako mai zuwa kan matsalar
  • Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya ce an taba gayyatar shugabannin tsaron, amma ba su samu damar zuwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaMajalisar Dattawa ta sake gayyatar dukkannin manyan hafsoshin tsaro domin bayyana a gabanta mako mai zuwa kan matsalar tabarbarewar tsaro a kasar.

Cikin wadanda aka gayyata akwai Mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, Shugaban rundunar sojin kasa, Janar Christopher Musa da shugaban rundunar sojin kasa, Janar Olufemi Oluyede.

Kara karanta wannan

"Jonathan ya yi bankwana da siyasa," PDP ta magantu kan fito da shi takara

Majalisa
Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro Hoto: Nuhu Ribadu/Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Dalilin majalisa na gayyatar shugabannin tsaro

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sauran shugabannin tsaron da aka gayyata sun hada da Shugaban rundunar sojin ruwa, Emmanuel Ogalla da Shugaban rundunar sojin sama, Hasan Abubakar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma an gayyaci Sufeto janar na ‘yan Sanda, Kayode Egbetokun; Darakta Janar na hukumar leken asiri (NIA), Mohammed Mohammed; da Darakta Janar na hukumar DSS, Adeola Ajayi.

Punch News ta ruwaito cewa yayin zaman majalisa na ranar Laraba, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce an taba gayyatar shugabannin, amma ba su samu damar zuwa ba.

Senate
Shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya bayyana damuwa kan rashin tsaro Hoto: The Senate President - Nigeria
Asali: Facebook

Ya ce zaman da aka sake shirya wa mako mai zuwa zai tattauna kan matsalolin tsaron da su ka addabi Najeriya tare da nemo hanyoyin gaggawa na shawo kansu.

Majalisar ta kuma bayyana damuwa kan zarge-zargen da ke nuna cewa wasu kungiyoyin kasa da kasa na daukar nauyin ‘yan Boko Haram a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta kai karar Akpabio ga kungiyar 'yan majalisun duniya

'Yan majalisa sun nemi karin tsaro a Binuwai

A gefe guda, Majalisar Dattawa ta bukaci hukumomin tsaro da su tura karin jami’ai domin dawo da doka da oda a jihar Binuwai.

Kiran ya biyo bayan hare-haren ‘yan bindiga da kisan gillar da aka yi a karamar hukumar Gwer ta Yamma a jihar bayan wata hatsaniya ta barke.

Wannan bukata ta biyo bayan amincewa da kudurin da Sanata Titus Zam (APC-Binuwai) ya gabatar a zaman majalisa na ranar Laraba a Abuja.

Zam, a cikin kudurinsa na gaggawa, ya bayyana cewa a ranar 10 ga watan Maris, an kai wani hari da ya yi sanadin mutuwar mutane hudu a yankin.

Majalisa na son a kawo karshen rashin tsaro

Shugaban majalisar ya ce sakamakon wannan hari, matasa sun fusata suka fito zanga-zanga kan ci gaba da kashe-kashen da ake yi wa jama’a da kuma gazawar gwamnati wajen kare su.

Sanatan ya bayyana cewa matasan da suka fusata sun banka wa ginin sakatariyar karamar hukumar wuta, tare da kona fadar basaraken yankin, gidansa na kansa.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Ɗan Majalisar da ya jagoranci dakatar da Sanata Natasha ya shiga matsala

Ya ce:

“Wannan yanayi ya kara karfafa gwiwar ‘yan bindiga tare da kara ta’azzara matsalar tsaro a jihar Binuwai da ma wasu sassa na kasar.”

Jami'an tsaro sun rufe zauren majalisar Ribas

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara, ya gamu da tangarɗa yayin da ya isa harabar majalisar dokoki domin amsa gayyatar da aka masa a ranar Laraba.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro da ke gadin majalisar ne suka kulle ƙofofin lokacin da ayarin motocin gwamnan ya isa zauren, sun ce ba a ba su izinin barinsa ya shiga ciki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng