Sojoji Sun Yi Musayar Wuta da 'Yan Bindiga a Hanyar Kaduna, An Samu Asarar Rayuka
- Dakarun sojin Fansan Yamma sun kashe ‘yan ta’adda uku a wani harin kwanton bauna a kusa da tsaunin Ngwagi, kan hanyar Kaduna-Abuja
- A yayin samamen, an kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, gidan harsasai takwas, harsasai 374 da kuma wasu kayayyakin abinci
- Babban kwamandan runduna ta 1 ya yaba da aikin sojojin, inda ya karfafa masu gwiwa kan ci gaba da yaki har sai an kawar da duka ‘yan ta’adda
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Rahotanni sun tabbatar da cewa an gwabza fada tsakanin sojoji da 'yan bindiga a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda aka samu asarar rayuka.
An ce dakarun Operation Fansan Yamma sun kashe uku daga cikin 'yan ta'addan a harin kwanton bauna da suka kai masu a kusa da tsaunin Ngwagi.

Asali: Twitter
Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a hanyar Kaduna
Rahoton Zagazola Makama da ya wallafa a shafinsa na X ya nuna cewa an gwabza fadan ne a kusa da Gwagwada, kan hanyar Kaduna-Kaduna da ke Chikun, jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan samun sahihan bayanai kan motsin 'yan ta'adda da masu tayar da kayar baya, dakarun soji suka kaddamar da farmakin cikin gaggawa, a cewar rahoton.
Rahoton ya ce sojojin sun isa wurin da ake zargin ‘yan ta’addan ke wucewa da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Talata, 11 ga Maris.
A nan ne suka kai musu samame ba zato ba tsammani, inda suka hallaka mutum uku daga cikin gungun ‘yan ta’addan da ke dauke da makamai.
Makaman da aka kwato a hannun 'yan ta'addar
A yayin wannan samame, dakarun soji sun kwato makamai da alburusai masu yawa, ciki har da bindigogi biyu kirar AK-47 da rumbun ajiyar harsasai takwas na bindigar AK-47.
Haka nan, sun samu damar kwato harsasai 374 masu tsayin 7.62mm x 39 da kuma wasu 88 masu tsayin 7.62mm x 54 (NATO).
Baya ga haka, an ce sojojin sun samu nasarar kwato wayar salula kirar Infinix, magungunan shaye-shaye, tufafi da kayayyakin abincin da ake sandararwa.
Janar Mayirenso ya shirya kawar da 'yan bindiga

Asali: Twitter
Babban kwamandan runduna ta 1 ta sojin Najeriya kuma kwamandan sashe na 1 na Operation Fansar Yama, Manjo Janar Mayirenso Lander David Saraso, ya yabawa dakarun soji bisa jajircewarsu da kwazonsu a fagen yaki.
Ya bukace su da kada su yi sako-sako, tare da ci gaba da kai farmaki har sai an kawar da dukkan ‘yan ta’adda da masu aikata laifi a yankin.
Manjo Janar Saraso ya jaddada cewa wannan yunƙuri zai tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin da ake fama da matsalar tsaro.
Abun fashewa ya tarwatse da 'yan sanda
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani abun fashewa da ake zargin nakiya ce ya tashi da jami’an ‘yan sanda uku a kan titin Maiduguri-Damaturu, jihar Borno.
Ana zargin cewa ‘yan ta’addan ISWAP ne suka dasa nakiyar, wadda ta jikkata jami’an RRS yayin da suke sintiri a kusa da Garin Kuturu da ke jihar.
Asali: Legit.ng