Gwamna Ya Kaɗu bayan Rasuwar Kawunsa kuma Sarki Mai Shekaru 100

Gwamna Ya Kaɗu bayan Rasuwar Kawunsa kuma Sarki Mai Shekaru 100

  • Bala Mohammed ya sanar da rasuwar kawunsa, Sarkin Alkaleri, Muhammadu Abdulkadir, wanda ya rasu yana da shekaru 100
  • Marigayin ya rasu bayan fama da doguwar jinya, an kwatanta Sarkin da mutum mai hikima da kuma kishin al'umma a rayuwarsa
  • Bayanai sun ce an shirya gudanar da sallar jana'iza yau Alhamis da karfe 10:00 na safe a fadar Sarkin Alkaleri da ke jihar Bauchi
  • Gwamnan ya yi addu'ar Allah jikansa da rahama, ya kuma ba iyali da al’umma hakurin jure wannan babban rashi da ka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, cikin alhini da baƙin ciki, ya sanar da rasuwar kawunsa, Alhaji Muhammadu Abdulkadir (Sarkin Alkaleri).

Marigayin ya rasu a yau Alhamis 13 ga Maris, 2025, yana da shekaru 100, bayan fama da doguwar jinya.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamnan Jigawa ya kai ziyara wajen raba abinci, ya gano abin mamaki

Gwamna ya yi alhinin rasuwar fitaccen Sarki a Najeriya
Gwamna Bala Mohammed ya yi jimamin rasuwar Sarkin Alkaleri wanda ya kasance kawunsa. Hoto: Mukhtar Gidado.
Asali: Facebook

Gwamna ya jero gudunmawar marigayi Sarkin Alkaleri

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren sadarwa, Mukhtar Gidado ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce marigayin ya kasance ginshiki kuma mutum mai hikima da kishin al’umma wanda ya ba da gudunmawa da ba zai musaltu ba a tarihin rayuwarss gaba daya.

A matsayinsa na Sarkin Alkaleri, ya taka rawa wajen kawo haɗin kai da cigaba a Alkaleri da ma wajenta.

Sanarwar ta ce:

“Cikin alhini da baƙin ciki ne nake sanar da rasuwar kawuna mai daraja, Alhaji Muhammadu Abdulkadir (Sarkin Alkaleri).
"Basaraken ya rasu ne a yau Alhamis 13 ga Maris, 2025, yana da shekaru 100, bayan fama da doguwar jinya da ya shafe lokaci yana yi."
Gwamna ya tafka babban rashi na kawunsa a Bauchi
Gwamna Bala Mohammed ya tura sakon ta'azziya bayan rasuwar Sarkin Alkaleri. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed.
Asali: Facebook

Gwamna ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Alkaleri

Gwamnan ya ce a matsayinsa na Sarkin yankinsa, ya ba da gudunmawa sosai wajen haɗa kan jama’a da kuma kawo cigaba a Alkaleri da kewayenta wanda al'umma da dama ke cin gajiya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zubar da hawaye a cikin taro, ya bayyana abin da ya sosa masa zuciya

“Marigayin ginshiki ne mai hikima da sadaukarwa ga al’umma, rayuwarsa ta nuna cikakken shugabanci da biyayya ga hidimar jama’a.
“A matsayinsa na Sarkin Alkaleri, ya taka rawa wajen haɗa kan jama’a da kuma kawo cigaba a Alkaleri da kewayenta,”
“Allah jikansa da rahama, ya kuma ba iyalansa da al’umma ƙarfin jure wannan babban rashi da ya girgiza mu."

- Bala Mohammed

Za a gudanar da sallar jana’iza yau Alhamis 13 ga watan Maris, 2025 da misalin karfe 10:00 na safe a fadar Sarkin Alkaleri.

Gwamna ya fadi dalilin gina coci a Bauchi

A baya, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ke gina wa da gyaran coci-coci a jihar Bauchi, domin tabbatar da adalci ga kowa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, bisa rasuwar Janar Jeremiah Useni da kuma Sheikh Hassan Jingir.

Gwamnan ya ce suna gina coci domin Kiristoci ma 'yan jihar ne, su na da hakkinsu kamar kowa, ya jaddada muhimmancin hadin kai da zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng