"Za a Yi Kokarin Hana Tinubu Cin Zabe," CUPP Ta Yi Hasashen me Zai Faru a 2027
- Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar CUPP, Mark Adebayo, ya bayyana cewa rashin haɗin kan jam'iyyun PDP da ADC zai ba APC nasara cikin sauƙi
- Maimakon siyasar kishin ƙasa, yawancin ƴan siyasar adawa a Najeriya suna siyasar son zuciya ne da neman abinci, a cewar Mark Adebayo
- Adebayo ya yaba da yadda tattalin arziƙin ƙasa ke samun ci gaba, amma ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da addabar ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar haɗin kan jam’iyyun siyasa (CUPP), Mark Adebayo, ya yi gargaɗi mai zafi ga manyan jam’iyyun adawa na ƙasar nan.
Adebayo ya bayyana cewa muddin jam’iyyun PDP, ADC da sauran su ba su haɗe wuri guda ba, to shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi nasara a zaɓen 2027 cikin sauki.

Source: Twitter
Kuskuren 'yan adawa gabanin 2027
A wata hira da ya yi da Abdulrahman Zakariyau, na jaridar Punch, Adebayo ya ce rashin tsayayyar akida da yawaitar rigingimun cikin gida ne suka maida ƴan adawa tamkar matattu.
Ya kawo misali da yadda jam’iyyar PDP ta ƙi amincewa da tsarin karɓa-karɓa a 2023, sannan ya yi gargaɗin cewa idan jam’iyyar ADC ma ba ta tsaya kyam wajen tsayar da ɗan takara mai karɓuwa kamar Peter Obi ba, to za ta fuskanci mummunar faɗuwa.
Adebayo ya bayyana cewa ƴan siyasar adawa da yawa suna yin siyasar "nemam abinci" ne, inda suke ficewa zuwa jam’iyya mai mulki don buƙatun kansu.
Ya soki yadda ƴan adawa suka koma amfani da kafofin sada zumunta kawai maimakon fita zuwa kauyuka da lunguna don wayar wa talakawa kai.
Dabarar jam'iyyar APC kan 'yan adawa
Sakaren yara labaran CUPP ya bayyana cewa:
"Jam'iyya mai mulki ta fahimci dabarun siyasa; tana gano ƙwararrun mutane ta ɗauke su aiki ko da kuwa sun taɓa sukarta. Amma ƴan adawa suna watsi da masu basira, suna yin siyasar nuna bambanci da son zuciya."
Ya jaddada cewa ba tare da ƙwaƙƙwarar hamayya ba, dimokuradiyyar Najeriya za ta raunana, wanda hakan na iya mayar da ƙasar zuwa tsarin jam'iyya guda.
Yayin da yake tsokaci kan mulkin shugaba Tinubu, Adebayo ya yarda cewa akwai alamun nasara a fannin tattalin arziƙi inda aka fara samun sauye-sauye masu kyau.

Source: Facebook
Gargadin CUPP ga PDP, ADC
Sai dai, ya bayyana cewa babban abin da ke damun sa shi ne rashin tsaro, wanda a cewarsa shi ne ginshiƙin kowane irin ci gaba. Ya ce kashe-kashe, garkuwa da mutane, da ayyukan ƴan bindiga suna ci gaba da tsorata ƴan ƙasa.
Adebayo ya jinjina wa jami'an tsaro dake sadaukar da rayukansu, yana mai kiran ƴan ƙasa da su ba su goyon baya ta hanyar tallafa wa iyalansu ta hanyoyi masu ɗorewa.
Ya gargaɗi ƴan adawa cewa muddin ba su gyara tsarin su na cikin gida ba, ba su daina nuna wariya ba, kuma ba su samar da tsarin da zai ba talakawa kwarin gwiwa ba, to nasarar Tinubu a 2027 za ta kasance tamkar shan ruwa.
ADC ta yi martani ga kalaman Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, ADC ta bayyana cewa kalaman Shugaba Bola Tinubu na cewa ba za a iya tsorata shi ba alamun nuna fargaba ne kawai a yanzu.
Halin ƙuncin rayuwa da rashin tsaro da ƴan Najeriya ke ciki sune dalilan da ya kamata su sanya shugaban ƙasar tsoron zaɓen 2027, in ji ADC.
Jam'iyyar ta zargi gwamnatin tarayya da rufe filayen taro domin hana ƴan adawa gudanar da harkokinsu na siyasa, abin da ta kira 'takurawa'.
Asali: Legit.ng


