Majalisa Ta Dauki Mataki kan Hare Haren Boko Haram da Suka Kashe Manyan Sojojin Najeriya

Majalisa Ta Dauki Mataki kan Hare Haren Boko Haram da Suka Kashe Manyan Sojojin Najeriya

  • Majalisar Dattawa ta waiwayi hare-haren da ƴan ƙungiyar ta'addanci na Boko Haram suka kai sansanonin sojoji a Borno
  • An yi umarni da a gudanar da bincike iri biyu, wanda ya haɗa da gano yadda ƴan ta'addan suka iya cutar da sojojin a sansanoninsu
  • A zaman majalisa na ranar Laraba, 23 ga watan Afrilu, 2026, an bukaci rundunar soji ta binciki zargin cutar da fararen hula yayin aiki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Majalisar Dattawa ta ba wa Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, tare da sauran shugabannin rundunonin tsaro umarni da su gudanar da cikakken bincike hare haren Borno.

An bukaci su yi bincike a kan harkokin aiki da kayan aiki bayan hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan sansanonin soji a Benisheikh da Monguno da ke jihar Borno State.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Majalisa ta ba sojoji umarni
Shugaban majalisar Dattawa Godswill Akpabio da mataimakinsa Barau Jibrin Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Channels TV ta wallafa cewa wannan mataki ya biyo bayan kudurin da majalisar ta amince da shi yayin zaman majalisa na ranar Laraba 22 ga watan Afrilu na shekarar 2027.

Majalisa ta ba da umarni kan harin Boko Haram

Jaridar The Nation ta wallafa cewa majalisa ta bukaci a yi nazari mai zurfi kan yadda hare-haren suka faru, daga ciki har da tantance wadatar kayan aiki da kuma bin ka’idojin aiki na rundunar soji.

Sanatoci sun kuma bukaci rundunar soji ta magance duk wani gibi da binciken zai gano, domin inganta tsaro da hana sake aukuwar irin wadannan hare-hare a nan gaba.

Haka kuma, majalisar ta jaddada bukatar bincikar zargin cutar da fararen hula yayin ayyukan soji, domin tabbatar da daukar alhaki da kare rayukan jama’a.

Yadda aka bijiro da kudirin a majalisa

Kudurin ya samo asali ne daga wata bukata ta gaggawa da Sanata Tahir Monguno ya gabatar, inda ya yi kira da a dauki matakin dakile hare-haren da mayakan Boko Haram ke kai wa sansanonin soji.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: ICIR ta fallasa 'boyayyun dalilan' Tinubu na tsige ministoci 2

Yayin gabatar da kudurin, Sanata Monguno ya nuna matukar damuwa kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar jami’an soja da dama.

Daga cikin wadanda suka rasu akwai Birgediya Janar Oseni Braimoh, Kanal Mohammed Isya, Kyaftin A.M. Esmat, Laftanar Kelvin Festus da wasu sojoji 13.

Harin Boko Haram a Borno ya kashe manyan sojojin Najeriya
Taswirar jihar Borno da ke fama da matsalolin ta'addanci Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya bayyana cewa hare-haren da ake ci gaba da kai wa Monguno da kuma Benisheikh da ke kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, na nuna cewa ‘yan ta’adda na kokarin raunana ayyukan soji.

Majalisar ta yaba da sadaukarwar da dakarun Najeriya ke yi a yaki da ta’addanci, amma ta yi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare kan sojoji da fararen hula na barazana ga tsaron kasa.

Sojojin Najeriya na samun horo

A baya, mun wallafa cewa rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa wasu jami'anta na karbar horo na musamman a Amurka a shirin yaki da ta'addanci.

NAF ta bayyana cewa da zarar jami'an sun gama samun horo za su dawo gida bakin aiki domin ci gaba da amfani da abubuwan da suka koya domin inganta tsaro.

Ta kuma bayyana irin horon da ake ba sojojin a jihar Ohio ta kasar Amurka domin su kawo sauyi a aikin soja idan suka dawo gida Najeriya wajen fatattakar ƴan ta'adda.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng