"Babu Wanda Zai Dawwama a Mulki," Gwamna Ya Ji Haushin Abin da Aka Masa a Majalisa
- Gwamna Siminalayi Fubara ya tunatar da ƴan Majalisar dokokin jihar Ribas cewa babu wanda zai dawwama kan karagar mulki a duniya
- Fubara ya yi maganar ne da yake martani bayan ƴan Majalisar sun hana shi shiga wurin da suke zama don sake gabatar da kasafin kuɗi
- Mai girma gwamnan ya ce yana iya bakin ƙokarinsa domin aiwatar da hukuncin kotun koli ba don komai ba sai don ci gaban al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya mayar da martani bayan an hana shi damar shiga majalisar dokoki domin gabatar da kasafin kudin 2025.
A jiya Laraba, jami'an tsaro suka rufe ƙofar shiga zauren Majalisar Dokokin Ribas na wucin gadi da ke Fatakwal yayin da Gwamna Fubara da tawagarsa suka isa wurin.

Asali: Facebook
Rigimar Fubara da Majalisar Dokoki

Kara karanta wannan
Wike ya kara rura wutar rikicin Rivers, ya fadi abin da zai faru idan an tsige Fubara
Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Fubara ya isa majalisar tare da tawagarsa, amma suka tarar da kofar shiga a kulle.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A baya, ‘yan majalisar sun ba Fubara wa’adin sa'o'i 48 ya gabatar da kasafin, wanda a da bangaren majalisa mai mambobi hudu da ke goyon bayansa suka amince da shi.
Sai dai kotun ƙoli ta ayyana mambobi 27 na tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, a matsayin halattattun ‘yan majalisar jihar.
Gwamna ya ji haushin rufe masa ƙofa
Da yake jawabi yayin kaddamar da asibitin Bori a karamar hukumar Khana, Fubara ya bayyana takaicinsa kan yadda ake sa siyasa a batun tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa ya bi duk matakan da suka dace domin warware matsalar, yana fatan ‘yan majalisar za su amince da hukuncin kotun koli.
Ya ce:
"Na yi kokari matuka don na tuntubi Kakakin Majalisa da sauran ‘yan majalisa. Ban ga dalilin da zai sa su musanta hakan ba.
"Na ma tura musu sakonni ta WhatsApp, na sanar da su cewa zan zo karfe 10:00 na safe domin gabatar da kasafin kudi. Wannan duk domin tabbatar da cewa ba a jefa jihar Ribas cikin matsala ba saboda da ni.”
Gwamna ya bar komai a hannun Allah
Gwamna Fubara ya ƙara da cewa abin takaicin shi ne yadda aka hana shi shiga majalisar, wai saboda bai sanar ba a hukumance.
A ruwayar Punch, Fubara ya ce:
“Ba komai, na bar komai a hannun Allah wanda ke ganin abin da ke ɓoye. Na sami labarin cewa wai na je ban sanar ba shi yasa nake amfani da wannan dama domin fayyace gaskiya.”

Asali: Facebook
A karshe, gwamnan ya ja hankalin ‘yan siyasa da su gane cewa komai da suke gani yana da iyaka, babu abin da zai dawwama a duniya.
"Ba wani abu da ke dawwama, duk wani mulki da ƙarfin iko yana karewa a karshe. Abu mafi muhimmanci shi ne yin abin da ya dace a mulki, ni dai ina iya bakin ƙoƙari na."
Me zai faru idana aka tsige gwamna?
A wani labarin, kun ji cewa ministan harkokin Abuja ya ce idan har Gwamna Simi Fubara ya aikata laifi, ba wani abu ba ne don Majalisar Dokoki ta tsige shi.
A wata zantawa da aka yi da shi, Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce babu abin da zai faɗu idan an tsige Gwamna Fubara daga kan mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng