Ana Wata ga Wata: Kalaman El Rufai Sun Jawo Masa Sabuwar Matsala daga Shiga SDP
- Jam'iyyar NNPP ba ta ji daɗin zargin da Nasir El-Rufai ya yi ba na cewa gwamnatin APC ta na da hannu a rikicin da ya addabe ta
- NNPP ta musanta zargin da tsohon gwamnan ya yi na cewa da hannun gwamnatin APC a korar da aka yi wa Rabiu Kwankwaso daga cikinta
- Jam'iyyar ta kuma ba El-Rufai wa'adi kan ya fito ya nemi afuwa ko kuma ta ɗauki matakin shari'a a kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ogun - Jam’iyyar NNPP ta yi wa Nasir El-Rufai martani kan zargin cewa gwamnatin APC na da hannu a rikicin cikin gida da ya addabe ta.
Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da hannu a rikicin cikin gida da ke addabar ta, da korar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da dakatar da Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce sakataren jam’iyyar na ƙasa, Oginni Sunday, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan za a iya tunawa, Mallam Nasir El-Rufai, wanda ya sauya sheƙa daga APC zuwa SDP a ranar Litinin, ya yi zargin cewa rikicin da ke faruwa a jam’iyyun LP, PDP da NNPP gwamnatin APC ce ta haddasa shi.
NNPP ta yi wa Nasir El-Rufai martani
Sai dai, Oginni Sunday ya ce abin takaici ne cewa El-Rufai, wanda bai daɗe da ficewa daga APC zuwa SDP ba, yana aikata abin da bai dace ba ta hanyar yin zarge-zarge marasa tushe balle makama kan shugabancin NNPP.
Ya bayyana cewa babu hannun gwamnatin tarayya a korar da aka yi wa Kwankwaso da kuma dakatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP.
"Shin wai gwamnatin tarayya ce ta umarci Kwankwaso da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da aka kora da su wawure kuɗin da aka tara na sayar da fom da gudunmuwar da aka samu domin zaɓen 2023?"
"Shin gwamnatin tarayya ce ta shigar da ƙorafi ga hukumar EFCC kan zargin sama da Naira biliyan 2.5 da ake yi wa Kwankwaso da muƙarrabansa a kwamitin gudanarwa?
- Oginni Sunday
Jam'iyyar NNPP ta ba El-Rufai wa'adi
Oginni ya ƙara da cewa jam’iyyar NNPP ta ba El-Rufai wa’adin awanni 48 da ya janye wannan magana tasa tare da fitowa ya bayar da haƙuri a fili.
Ya ce idan bai yi hakan ba za su ɗauki matakin shari’a a kansa bisa zargin ɓata sunan shugabancin jam’iyyar.
Gwamna ya musanta shirin bin El-Rufai zuwa SDP
A baya rahoto ya zo cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya musanta batun cewa zai bi Nasir Ahmad El-Rufai zuwa jam'iyyar SDP.
Gwamna Alia ya bayyana cewa wannan jita-jitar da ake yaɗawa babu komai a cikinta face tsantsagwaron ƙarairayi.
Ya yi nuni da cewa ko kaɗan bai da shirin ficewa daga jam'iyyar APC wacce ya samu kujerar gwamna a ƙarƙashinta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng