2027: Kano da wasu Jihohin Arewa 7 da Majalisa ke Son Haramta wa Yin Kamfen
- Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnati ta yi duba yiwuwar dakatar da harkokin siyasa a jihohi takwas na Arewacin Najeriya
- A zaman majalisar, Sanata Abdul Ningi ya ce rashin tsaro ya zama barazana ga kasa baki daya, ba wai yankuna kaɗai ba
- Haka kuma Majalisar Tarayyar ta nemi a gaggauta ceto mutane 416 da ake ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace a jihar Borno
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa kuma masu tsauri a jihohin da ke fama da rashin tsaro.
Daga cikin matakan da ake son gwamnati ta dauka akwai yiwuwar dakatar da dukkanin harkokin siyasa a wasu jihohi takwas na Arewa, sakamakon yadda matsalar tsaro ke kara kamari a sassan kasar.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan kira ya biyo bayan kudirin da Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya gabatar yayin zaman majalisa.
Majalisa na son a saka takunkumin kamfen
Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a dauki matakin da ya dace a jihohin da ke kuka da rashin tsaro.
The Cable ta rahoto shi yana cewa:
"Shugaban majalisa, ba za mu ci gaba da tunanin cewa saboda muna Abuja ne wannan abu (rashin tsaro) ba ya shafar mu ba.”
Ya kara da cewa:
“Daya daga cikin abubuwan da ya kamata mu yi, kuma ina so mu dauki wannan batu da muhimmanci, shi ne ko dai mu dakatar da dukkannin harkokin siyasa a fadin kasa ko kuma mu mai da hankali kan jihohi kamar Borno, Plateau, Bauchi, Binuwai, Neja, Sakkwato, Kebbi da wasu sassan Kano.”

Kara karanta wannan
"Kada ku bar Turawa su yaudare ku": Gumi ya shawarci gwamnati kan sulhu da ƴan ta'adda
Dalilin Sanatan na neman takunkumin kamfen
A cewarsa, ya zama dole a dakatar da harkokin siyasa a wadannan yankuna har sai an tabbatar da cewa an shawo kan matsalar tsaron da ake fama da ita.
Ningi ya bayyana cewa:
"Ba mu magance wannan matsalar rashin tsaro yadda ya kamata. Kuma ba na zargin kowa. Ba za mu rika zuwa nan kullum muna kuka ba.”
Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar karuwar hare-haren ‘yan Boko Haram a Arewa maso Gabas, daga ciki har da kai hare-hare kan sansanonin sojoji da kuma barazanar da suke yi kan yunkurin ceto mutanen da aka sace

Source: Facebook
A wani kuduri mai nasaba da wannan batu, Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta kara kaimi wajen ceto mata, yara da tsofaffi 416 da Boko Haram ta sace.
Kudurin ya biyo bayan nazarin wani muhimmin batu mai taken bukatar dakile hare-haren Boko Haram kan sansanonin sojoji, wanda Sanata Tahir Monguno ya gabatar tare da hadin gwiwar Ali Ndume da Kaka Lawan.
Majalisa ta magantu kan harin Boko Haram
A baya, kun samu labarin cewa Majalisar Dattawa ta waiwayi hare-haren da ƴan ƙungiyar ta'addanci na Boko Haram suka kai sansanonin sojoji a Borno.
An yi umarni da a gudanar da bincike iri biyu, wanda ya haɗa da gano yadda ƴan ta'addan suka iya cutar da sojojin har cikin manyan sansanoninsu.
A zaman majalisa na ranar Laraba, 23 ga watan Afrilu, 2026, an bukaci rundunar soji ta binciki zargin cutar da fararen hula yayin aiki kamar yadda ake samun labari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

