El Rufai Ya Bayyana Yadda Suka Yi da Buhari kan Batun Ficewarsa daga APC zuwa SDP

El Rufai Ya Bayyana Yadda Suka Yi da Buhari kan Batun Ficewarsa daga APC zuwa SDP

  • Malam Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa da sanin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya fice daga APC zuwa SDP
  • Tsohon gwamnan Kaduna ya ce ya je har gida, ya faɗa wa Buhari cewa ga shirin da yake yi na barin APC kuma ya amince da hakan
  • Ya ce Buhari ne mai gidansa na farko a siyasa kuma ba ya ɗaukar kowane irin mataki tun yana gwamna sai ya tuntuɓe shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya tuntuɓi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhaɗi kafin ya bar APC zuwa SDP.

El-Rufai ya ce bai bar jam'iyyar APC ba sai da ya shawarci Buhari kuma ya amince da hakan sannan ya fito ya sanar da duniya cewa ya sauya sheka zuwa SDP.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Kalaman El Rufai sun jawo masa sabuwar matsala daga shiga SDP

Buhari da El-Rufai.
Malam Nasir El-Rufai ya ce da amincewar Buhari ya bar APC Hoto: @Elrufai
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya yi wannan bayani ne a wata hira da sashin Hausa na BBC ya yi da shi, wanda aka watsa da safiyar ranar Alhamis, 13 ga watan Maria, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufai ya raba gari da APC

Idan ba ku manta ba Nasir El-Rufai ya ce ya yanke shawarar ficewa daga APC ne saboda jam'iyyar ta sauka daga tubalin da suka gina ta a kai.

Ya kuma tabbatar da cewa zai yi ƙoƙarin jawo hankalin manyan ƴan adawar kasar nan zuwa SDP domin su haɗu su yaƙi APC a zaɓuka masu zuwa.

Buhari ya amince da matakin El-Rufai

A hirar da aka yi da shi, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa bai bar APC ba sai da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince kuma ya sa masa albarka.

"Da saninsa na bar APC. Sai da na je ranar Juma’a na faɗa masa cewa zan bar jam’iyyar. Babu wani abu da nake yi a siyasa ba tare da na sanar da shi ba,"

Kara karanta wannan

"Da shi muka shirya yaƙar Atiku," Wike ya tona asirin gwamna a Arewacin Najeriya

- in ji shi.

Malam El-Rufai ya ce tun lokacin da yake gwamna, duk wani muhimmin mataki da zai dauka sai ya fara neman shawarin Buhari kafin ya zartar da shi.

“Lokacin da zan naɗa kwamishinoni a Kaduna, sai da na kai wa Buhari jerin sunayensu domin ya duba ko akwai wanda ya taɓa zaginsa.
Bayan ya duba ya yi dariya ya ce ba matsala, Allah ya yi albarka,”

- in ji shi.

Malam Nasir.
El-Rufai ya ce Buhari ne ubangidansa na farko a siyasa Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: UGC

"Buhari ne mai gida na" - El-Rufai

Dangane da ubangidan siyasa kuma, tsohon gwamnan ya ce ba shi da ubangidan siyasa amma akwai mutanen da yake mutuntawa kuma yake neman shawarinsu.

"Mene ne ubangida? Ni ba ni da ubangida a siyasa, amma ina da mutane da nake shawara da su. Duk wani abu da zan yi, sai na tuntube su. Idan suka ce in dakata, zan dakata.”

Malam Nasir El-Rufai ya kara da cewa Muhammadu Buhari ne mutumin farko da yake dauka a matsayin shugaba kuma jagora a siyasarsa.

Kara karanta wannan

Bayan rasa El-Rufai, gwamnatin Tinubu ta fadi dan takarar shugaban kasa da zai dawo APC

"Mai gidana na farko shi ne Muhammadu Buhari. Sauran kuma ba zan ambace su ba saboda idan na faɗi sunayensu, mutane za su matsa musu,” in ji shi.

Rikici ya ɓarke a SDP daga zuwan El-Rufai

A wani labarin, kun ji cewa rikici ya ɓarke a jam'iyyar SDP reshen jihar Kogi awanni ƙalilan bayan sauya shekar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Shugaban SDP na jihar, Moses Peter Oricha, ya ce ya samu labarin waus na shirin ɓallewa su kafa tsaginsu a jam'iyyar, ya buƙaci a kauracewa taron da suka shirya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262