Jami’in Hukumar NIS Ya Tsunduma a Matsala, An Kama Shi Ya Damfari Gwamnati N17.6m
- Hukumar ICPC ta gurfanar da wani jami’in shige da fice, Abubakar Mohammed Aseku, bisa zargin karɓar albashi daga ma’aikatu uku a lokaci guda
- Aseku yana fuskantar tuhuma kan karɓar N17.6m daga ma’aikatar ilimin Nasarawa, hukumar DPR da hukumar shige da ficen Najeriya (NIS)
- An gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Binta Dogonyaro a Abuja, inda kotu ta ba da shi beli tare da dage shari’a har zuwa 29 ga watan Afrilu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta gurfanar da wani jami’in hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) bisa zargin karɓar albashi daga ma’aikatu uku na gwamnati.
Ana zargin Abubakar Mohammed Aseku, da karɓar albashin N17.6m daga ma’aikatu daban-daban a wani tsawon lokaci, lamarin da ya sabawa dokokin aikin gwamnati.

Asali: Twitter
Ana zargin jami'in NIS ta karbar albashi 3
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Aseku, wanda ke da mukamin mataimakin sufritanda na shige da fice (ASI), yana karɓar albashi daga ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha ta jihar Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga haka, an gano cewa yana kuma karɓar albashi daga hukumar kula da man fetur (DPR), yayin da yake karbar albashinsa a hukumar shige da fice (NIS).
An gurfanar da wanda ake zargi a gaban Mai shari’a Binta Dogonyaro ta Babbar Kotun Tarayya da ke Apo, birnin Abuja, ana tuhumarsa da zargin wannan badakala.
Aseku yana fuskantar tuhuma tara da suka shafi cin hanci, rashawa da kuma amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, kamar yadda kakakin ICPC, Demola Bakare, ya bayyana.
Kudin da ake zargin jami'in ya karba
A cewar ICPC, jami'in na NIS ya karɓi Naira miliyan 4.2 a matsayin albashi daga ma’aikatar ilimi ta Nasarawa a shekarar 2015, duk da cewa a lokacin yana aiki da NIS.
Haka kuma, ana tuhumarsa da karɓar Naira miliyan 13.4 daga hukumar DPR tsakanin shekarar 2018 zuwa 2019, yayin da yake ci gaba da aiki a matsayin jami’in NIS.
ICPC ta kara da cewa Aseku, wanda ke aiki a matsayin jami’in biyan albashi a NIS, ya taimaka wajen biyan albashin wasu mutane bakwai da ba a cikin ma’aikatan NIS suke ba.
Kotu ta bayar da belin ASI Aseku

Asali: UGC
Jaridar PM News ta rahoto cewa, da aka karanta masa tuhume-tuhumen da ake yi masa, Aseku ya musanta aikata duk wani laifi da ake zarginsa da shi.
Lauyansa, Basil Hemba, ya roki kotu da ta bar shi a kan tsarin belin da wata kotun Abuja da ke Maitama ta bayar a baya, domin ya ci gaba da kasancewa a waje.
Mai Shari’a Dogonyaro ta amince da wannan bukata, inda ta sake shi bisa ga sharuɗɗan belin da kotun Maitama ta bayar a baya.
An daga sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu domin ci gaba da bincike da kuma gabatar da kwararan shaidu.
An dakatar da jami'in NIS kan rashawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar shige da fice ta kasa ta dakatar da jami'inta, Okpravero Ufuoma, bayan bidiyonsa ya karade kafafen sada zumunta.
A bidiyon da ya yadu a shafukansa sada zumunta, an nuna Ufuoma yana kokarin karbar cin hanci daga matafiya a filin jirgin sama, lamarin da ya sa aka yi tir da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng