Mata Masu Karuwanci Sun Maka Ministan Tinubu a Kotu, An Yanke Hukunci da Azumi
- Babbar Kotun Tarayya ta yi watsi da karar da wata kungiyar kare hakkin ɗan adam ta shigar a madadin mata masu karuwanci a titunan Abuja
- Masu karar dai sun bukaci kotun ta hana ministan Abuja, Nyesom Wike da hukumar kula da mahalli kamawa da gurfanar da karuwai a kotu
- Mai shari'a James Omotosho ya kori karar gaba ɗaya bisa rashin cancanta a zaman kotu na ranar Laraba, 12 ga watan Maris, 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar kotun tarayya ta yi fatali da ƙarar da mata masu zaman kansu, waɗanda ke sana'ar karuwanci a titin Abuja suka shigar da ministan birnin tarayya, Nyeson Wike.
Matan masu zaman kansu sun shigar da wannan ƙara ne ta hannun wata ƙungiya mai rajin kare haƙƙoƙin kananan yara da mata.

Kara karanta wannan
Rikicin maida mai martaba sarki kan sarauta ya zo ƙarshe, kotun ƙoli za ta yi hukunci

Asali: Twitter
Mai Shari'a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yi watsi da ƙarar da ƙungiyar kare haƙkin mata da yaran ta shigar yau Laraba, Channels tv ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ƙarar karuwan ta ƙunsa
Tun farko dai ƙungiyar, a madadin karuwan Abuja, ta nemi a hana Wike, da Hukumar Kare Muhalli ta Abuja (AEPB) kamawa da gurfanar da mata masu zaman kansu da ake zargi da sana'ar karuwanci.
Masu ƙarar sun gabatar da ƙorafinsu gaban kotu ne bisa ga tanadin dokar kare haƙƙin ɗan adam ta 2009.
Sun buƙaci kotu ta fayyace masu ko ayyukan AEPB ƙarƙashin sashe na 6 na Dokar AEPB ta 1997 sun haɗa da tsare, kama, da gurfanar da mata da ake zargi da yin aikin karuwanci a titunan Abuja.
Sun nemi kotu ta ayyana cewa tuhumar da AEPB ke yi wa karuwai a gaban kotun tafi-da-gidanka, har take kiran matan da aka kama da suna 'kayayyaki' kuma ake ɗaukar jikinsu a matsayin 'hajar sayarwa', a matsayin wanda ya saɓa doka.
A cewar masu ƙarar tuhumar ta saba wa tanadin sashe na 42 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa garambawul.

Asali: Facebook
Kotu ta yanke hukunci kan ƙarar karuwai
A hukuncinsa, Mai Shari'a Omotosho ya bayyana cewa ƙarar da ƙungiyar ta shigar a madadin matan da ke karuwanci ba ta da inganci ƙarƙashin ka'idojin Dokar Kare Haƙƙin Dan Adam ta 2009.
Ya ce, ko da a ce ƙarar tana da inganci, bukatun da masu ƙarar suka nema ba za a iya amincewa da su ba. Saboda haka, kotun ta yi watsi da ƙarar bisa rashin cancanta.
Wannan hukunci ya jaddada cewa ƙungiyoyi ba za su iya shigar da ƙara kan haƙƙin dan adam a madadin wasu ba tare da waɗanda abin ya shafa suna cikin ƙarar ba.
Haka kuma, ya nuna cewa dole ne a sami hujjoji masu ƙarfi da ke nuna cewa an keta haƙƙin dan adam kafin a iya ci gaba da irin wannan shari'a.
Minista ya yi rusau a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya jagoranci rushe wasu gidaje a unguwar Gishiri da ke cikin babban birnin tarayya.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun yi ƙoƙarin hana rushe-rushen ta hanyar rufe hanya don dakatar da motocin buldoza da ke rushe gidajensu amma yan sanda suka tarwatsa su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng