Yaki Ya Sauya Salo: Trump Ya Fusata, Ya Umarci Tarwatsa Jiragen Iran a Mashigar Hormuz
- Shugaban Amurka Donald Trump ya umurci sojojin ruwa su harbe duk jirgin Iran da ke shimfida bam a mashigin Hormuz, yana mai jaddada cikakken iko
- Ya ce babu wani jirgi da zai shiga ko fita ba tare da amincewar rundunar ruwa ta Amurka ba, yayin da ake kokarin tsaftace bam din ruwa
- Iran ta kama wasu jiragen ruwa biyu, yayin da Amurka ke ci gaba da sa takunkumi da tsauraran matakai, lamarin da ke kara dagula tattaunawar zaman lafiya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarni mai tsauri ga rundunar sojojin ruwa kasarsa.
Trump ya umurce su da su harbe duk wani jirgin Iran da ke shimfida bam a mashigin Hormuz da ake taƙaddama a kai.

Source: Getty Images
Amurka ta sha alwashi kan mashigar Hormuz
Rahoton Al Jazeera ya ce Trump ya jaddada cewa Amurka na da cikakken iko a yankin fiye da yadda ake tunani.
Trump ya ce babu wani jirgi da zai shiga ko fita ba tare da amincewar rundunar ruwan Amurka ba, yana mai cewa an rufe mashigar sosai har sai Iran ta amince da yarjejeniya.
Wannan mataki ya biyo bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, bayan sojojin Iran sun kai hari kan jirage uku tare da kama biyu.
Iran ta cafke wasu jiragen Amurka
Kafofin yada labaran Iran sun bayyana sunayen jiragen da aka kama, yayin da wani jirgi ya tsere.
Kamfanin Technomar ya tabbatar da kama daya daga cikin jiragen a yankin wanda ya jawo maganganu dalilin haka.
Wannan shi ne karon farko da Iran ta fara kame jiragen ruwa tun bayan fara yakin, matakin da ta ce ta dauka ne a matsayin martani ga kame jiragenta da Amurka ke yi.
Iran ta ce tana da iko da mashigin Hormuz, tana kokarin kakaba kudin wucewa ga jiragen ruwa, matakin da Trump ya ce zai hana ta hanyar kakaba takunkumi.

Source: Getty Images
Yadda Amurka ta hana jirage 31 wucewa
Rundunar Amurka ta ce ta hana jirage 31 wucewa s bayan fara takunkumin, tare da kama wani jirgi dauke da mai daga Iran a tekun Indiya, cewar rahoton The Economic Times.
Ana ci gaba da wannan rikici ne yayin da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran ke fuskantar tsaiko, duk da kokarin Pakistan na shiga tsakani.
Mai magana da yawun Iran ya zargi Amurka da aika sakonni masu rikitarwa, yana mai cewa matsalar ba daga bangaren Iran ba ce, sai dai halayyar Washington.
Amurka ta magantu kan tsagaita wuta
A wani labarin, an ji cewa Fadar shugaban kasar Amurka, White House, ta musanta rahotannin da ke cewa kwanaki uku zuwa biyar aka kara a wa'adin taagaita wuta.
Ta ce Shugaba Donald Trump ne kadai ke da ikon kayyade lokacin tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran kuma bai yi hakan ba a yanzu.
Fadar White House ta kuma jaddada cewa har yanzu Amurka na dakon amsa daga kasar Iran kan sharuddan yarjajeniyar zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

