Takarar 2027: Manyan 'Yan Siyasa Sun Raka Yusuf Buhari wajen Gwamna Radda
- Masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Daura sun gabatar da Yusuf Muhammadu Buhari ga gwamna Dikko Radda na jihar Katsina
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake maganar cewa ya dace Yusuf Buhari ya tsaya takarar Majalisar wakilai a zaben 2027 da ke tafe
- A yayin taron, gwamna Dikko Radda ya bukaci a cigaba da bin tsari da tuntubar jama’a yayin da ake cigaba da shirye-shiryen zaben 2027
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya karbi bakuncin masu ruwa da tsaki daga mazabar tarayya ta Daura–Sandamu–Mai’adua a gidan gwamnati da ke Katsina.
Tawagar ta gabatar da Yusuf Muhammadu Buhari a matsayin zabin su domin wakiltar su a majalisar wakilai, bayan gudanar da tattaunawa mai fadi a tsakanin al’umma.

Kara karanta wannan
Bayan 'sallamar' mutum 2, an kara samun ministan da ya yi murabus a gwamnatin Tinubu

Source: Facebook
Bayanin gwamna Dikko Radda
Mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa Dikko Radda ya jaddada muhimmancin ladabi, bin tsari da tuntubar jama'a a harkokin siyasa.
“Siyasa na bukatar hakuri, tsari da tuntubar jama'a. Ku shiga cikin al’umma, ku ziyarci mazabu da kananan hukumomi, ku tuntubi shugabannin siyasa, sannan ku bi hanyoyin da suka dace wajen neman goyon bayan jama’a,”
In ji gwamnan.
Daily Trust ta rahoto ya kara da cewa:
“Hakan na nufin kara hulda da jama’a da karfafa dimokuradiyya tare da tabbatar da cewa duk wani buri ana bi da shi cikin gaskiya da mutunta tsari,”
Tarihin Dikko Radda a siyasa
Gwamna Radda ya tuna da tafiyarsa ta siyasa na sama da shekaru 20, ciki har da aikinsa a matsayin babban hadimi a zamanin tsohon gwamna Aminu Bello Masari.
Dikko Radda ya kuma bayyana cewa marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a a matsayin Darakta-Janar na SMEDAN.

Kara karanta wannan
2027: Shugaba Tinubu ya ci gaba da sukar 'yan adawa, ya bayyana 'yaudarar' da suke yi
Ya ce yana da alaka mai karfi da gadon siyasa da iyalan marigayi Buhari, yana mai jaddada cewa ba zai taba kauce wa dabi’un da ya tsaya a kai ba.
Gwamnan ya tabbatar da cewa Daura, Sandamu da Mai’adua har yanzu wurare ne da jam’iyyar APC ke da karfi, tare da danganta hakan da tasirin Buhari.
Ya kuma bayyana cewa tsarin dimokuradiyya na Najeriya ya ba kowane dan kasa damar neman mukamin zabe, yana mai cewa takarar Yusuf Buhari ya samo asali ne daga shawarar al’umma ba daga gare shi ba.
Bayanin masu ruwa da tsaki
Sarkin gundumar Dumurkul, Alhaji Musa Haro, ya yabawa gwamnan kan jagorancinsa da ayyukan ci gaba a fadin jihar, yana mai cewa bayan tuntuba mai zurfi, sun amince da Yusuf Buhari a matsayin zabin su.
Haka kuma, ministar al’adu da yawon bude ido, Hannatu Musa Musawa, ta bayyana taron a matsayin alamar hadin kai a siyasa.

Source: Facebook
Bayanin Yusuf Buhari kan 2027
Rahotanni sun nuna cewa Yusuf Muhammadu Buhari ya gode wa masu ruwa da tsaki da gwamnan bisa goyon bayan da suka nuna masa.
“Ba zan yi wasa da yarda da ku ka nuna mani ba. Zan yi kokari wajen ci gaba da hidima kamar yadda aka saba tare da aiki da matasa domin gina makoma mai kyau ga mazabar mu,”
- In ji shi.
Wadanda suka halarci taron sun hada da kakakin majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, sakataren gwamnatin jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari, da sauran manyan jami’an gwamnati.
Ministan Tinubu zai yi takarar gwamna
A wani labarin, mun kawo muku cewa Ministan makamashi na kasa, Bayo Adelabu ya kudiri aniyar takarar gwamna a zaben 2027 mai zuwa.
An samu bayanai game da haka ne bayan ganawar Adelabu da shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa ranar Talata, inda ya mika wani rahoto.
Adelabu ya nemi gwamnan Oyo a 2019 da 2023 amma bai samu nasara ba, a wannan karon, ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki don neman dacewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
