An Ware Talakawan Najeriya Miliyan 68 domin ba Su Tallafin Kudi
- Rahotanni na nuni da cewa hukumar NASSCO ta ce ta tantance mutane miliyan 68 da ke fama da talauci a Najeriya
- Kundin da aka tattara bayanan talakawan ya nuna cewa ya kunshi gidaje miliyan 19 a jihohi 36 da birnin Abuja
- Hukumar NASSCO ta fitar da rahoton ne da ake kokarin amfani da bayanan domin rabon tallafin CCT ga mabukata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar jin kai ta NASSCO ta bayyana cewa ta riga ta tantance mutane miliyan 68 da ke fama da talauci a cikin kundin tallafin kasa (NSR).
Rahotanni sun nuna cewa wadannan mutanen sun fito ne daga gidaje miliyan 19 da ke fadin Najeriya, ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
Bayan hallaka jama'a da karbe kudin fansa, mugun 'dan ta'adda ya gamu da karshensa

Asali: Facebook
Jaridar Tribune ta wallafa cewa hukumar ta ce shirin na da nufin bai wa gwamnati cikakken bayani domin tsara daidaitattun shirye-shiryen rage talauci da bayar da tallafi ga mabukata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kokarin gwamnati na samar da tallafi
Shugabar NASSCO, Funmi Olotu, ta bayyana cewa kundin tallafin zai taimaka wajen tabbatar da cewa tallafin gwamnati yana isa ga wadanda suka cancanta.
Funmi Olotu ta ce:
“Manufarmu ba kawai bayar da taimako ba ce, sai dai samar da tsarin dindindin da zai ba da damar ceto iyalai da al’umma daga wahalhalun yau da kullum.”
Shugabar ta kara da cewa hukumar ta himmatu wajen tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan shirye-shiryenta, musamman na rabon kudin CCT ga talakawa.
Wasu sun koka kan raba tallafin CCT
Duk da kokarin gwamnati, rahoton Premium Times ya nuna cewa wasu ‘yan Najeriya sun bayyana damuwa kan yadda ake rabon tallafin CCT na N25,000 ga mabukata.
Wani tsohon mamba na shirin N-Power daga yankin Gwagwalada a Abuja, Dantala Ahmed, ya ce tsarin rabon kudin a baya ya fi na yanzu gaskiya.
Dantala Ahmed ya ce:
“A shekarar 2019 an ba mu kudin hannu-da-hannu.
"Jami’an gwamnati sun zo har Gwagwalada suka tara mu a wuri guda, inda aka duba sunayenmu a cikin rijista kafin a ba mu kudi.”
Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu, an daina bayani a fili kan yadda ake rabon kudin, illa kawai sanarwar da ake gani a kafafen sada zumunta.
Wasu na ganin an inganta shirin tallafin
A daya bangaren, wani mai amfana da shirin CCT daga yankin Kpako a karamar hukumar Suleja ta jihar Neja, Mohammed Awwal, ya ce tsarin rabon kudin yanzu yana tafiya bisa gaskiya.
Mohammed Awwal ya ce:
“Tsarin ya zama na zamani, domin jami’ai na zuwa mazabu domin rajistar wadanda suka cancanta ta amfani da lambar shaidar kasa (NIN).”
Ya kara da cewa amfani da fasaha a tsarin ya taimaka wajen rage matsalolin satar kudi da rashin adalci a rabon tallafin ga mabukata.

Asali: Twitter
Kamfani zai samar da ayyuka ga matasa
A wani rahoton, kun ji cewa matasa akalla 45,000 ne za su samu aiki a wani kamfanin siminti da ake shirin ginawa a jihar Kebbi.
A makon da ya wuce gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kulla yarjejeniyar kafa kamfanin simintin a jihar Kebbi domin habaka tattali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng