Latest
Shahararrun mawakan Kannywood, Adamu Hassan Nagudu da Yusuf Karkasara sun sauya sheka daga NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta hannun Barau Jibrin.
Wani abin fashewa da ake zargin nakiya ne ya tashi a Borno, inda ya raunata ‘yan sanda uku, yayin da ‘yan bindiga suka kashe yara shida da ke kiwo a jihar Kogi.
'Yan bindiga sun kafa sansani a Bakori, inda suke kai hare-hare. An rahoto cewa suna kokarin mamaye Tafoki, Faskari, Funtua da Danja, inda jama'a ke tserewa.
Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana cewa 'yan majalisar dokokin jihar na da hurumin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya bayyana yadda suka tsara yaƙar Atiku Abubakar tare da Gwamna Bala Muhammed na Bauchi amma ya ci amanarsu a zaɓen 2023.
Bayan rasa Nasir El-Rufai, hadimin shugaba kasa, Daniel Bwala ya ce dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi zai bar jam'iyyarsa ya koma APC kafin zaben 2027.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dauko matasa ya ba su mukamai a cikin gwamnatinsa. Gwamna Mai Mala Buni ya nada matasa 200 a matsayin hadimansa.
Yan bindigar da suka yi garkuwa da ma'aikata kwararrun masu binciken ƙasa a jihar Ondo sun sake su bayan an lale masu Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa.
Bayan alaƙa ta yi tsami tsakanin Nasir El-Rufai da gwamnatin Bola Tinubu da APC, tsohon gwamnan ya tattara komatsansa zuwa jam'iyyar adawa da SDP.
Masu zafi
Samu kari