Latest
An shiga jimami a jihar Delta bayan rasuwar tsohon gwamnan soja, Manjo-Janar Paul Ufuoma Omu, ya rasu yana da shekara 84 a duniya. Iyalansa sun fitar da sanarwa.
Hon. Mike Dio Jen ya yi murabus daga kujerar ɗan Majalisar dokokin jihar Taraba domin karɓar muƙamin kwamishina da Gwamna Agbu Kefas ya naɗa shi.
Majalisar Zartarwar Kano ta amince da Naira biliyan 51.5 don gudanar da ayyukan more rayuwa, ciki har da gyaran tituna da sabunta wutar lantarki.
Wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun sace wani basarake dauke da makamai a jihar Benue. 'yan sanda, sojoji, da wasu jami'an tsaro sun shiga daji kokari ceto shi.
Fitaccen matashin dan siyasa, Musa Azare ya ki karɓar mukamin SSA da gwamnan Bauchi ya ba shi, yana mai cewa zai fi amfani idan ya ci gaba da aikinsa na shari’a.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Farfesa Peter Ogban kan magudin zabe da ya yi don Godswill Akpabio bisa canja sakamako.
Sarakunan gargajiya da dama sun fuskanci dakatarwa daga gwamnonin jihohinsu tun watan Janairu 2025 zuwa yanzu saboda zarge-zarge na cin hanci da rashin adalci.
Jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya karbi wasu 'yan APC da suka sauya sheka a gidan shi da ke Abuja. Kwankwaso ya gana da jakadan tarayyar Turai.
Bayan takwaransa na Delta, Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya ce akwai yiwuwar sauya shekarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC na nan tafe kafin 2027 mai zuwa.
Masu zafi
Samu kari