ADC Ta Samu Karuwa a Kano, 'Yan Majalisar NNPP Sun Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar
- Jam'iyyar ADC mai adawa ta sake samun tagomashi bayan wasu 'yan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Kano sun sauya sheka zuwa cikinta
- 'Yan majalisar wakilan guda hudu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC ne bayan sun fice daga NNPP wadda suka lashe zabe a karkashinta
- Sauya shekar dai ta sanya yawan 'yan majalisar da jam'iyyar ADC ke da su sun karu bayan da a kwanakin baya wasu suka sauya sheka zuwa cikinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Abuja, tarayyar Najeriya - Mambobin majalisar wakilai hudu daga Kano sun fice daga jam’iyyar NNPP mai adawa.
Mambobin majalisar wakilan ta Najeriya sun sanar da sauya shekarsu zuwa jam’iyyar ADC bayan ficewa daga NNPP.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta wasikun sauya shekarsu.
'Yan majalisar NNPP sun koma ADC
Tajudeen Abbas ya karanta wasikun sauya shekar ne yayin zaman majalisar na ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun 2026.
’Yan majalisar su ne Sani Wakili (mazabar Minjibir/Ungogo), Muktar Zakari (mazabar Tarauni), Umar Datti (mazabar Kura/Madobi/Garun Mallam), da Abdulhakeem Ado (mazabar Wudil/Garko).
Wasu 'yan majalisa sun koma APC
Kabiru Amadu, wanda aka fi sani da Maipalace, mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta jihar Zamfara, da Emeka Chinedu (mazabar Ahiazu Mbaise/Ezinihitte, Imo), su ma sun koma jam’iyyar APC daga PDP.
’Yan majalisar wakilan sun bayyana rikicin cikin gida a tsofaffin jam’iyyunsu a matsayin dalilin sauya shekar tasu, jaridar Leadership ta kawo labarin.
Jam'iyyar ADC na samun karuwa
Jam’iyyar ADC ta samu karuwar ‘yan majalisa da dama a makonnin baya-bayan nan gabanin zaben shekarar 2027.
A ranar Talata, Thaddeus Attah (mazabar Eti-Osa, Legas), Usman Zubairu (mazabar Birnin Gwari/Giwa, Kaduna), da Sani Noma (mazabar Argungu/Augie, Kebbi) sun fice daga jam’iyyar LP da APC zuwa ADC, bi da bi.
Sauya shekar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun fara nuna alamun haɗa kai a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar ta ADC domin fuskantar zaɓen 2027.

Source: Facebook
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso dai shi ma ya bi sahun masu shiga jam'iyyar ADC bayan ya raba gari da NNPP wadda a baya yake matsayin jagoranta na kasa.
Sauya shekar dai na da nasaba da shirye-shiryen da 'yan siyasa ke yi na tunkarar babban zaben shekarar 2027 da ke tafe.
'Dan majalisar wakilai daga Kano ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Majalisar wakilan Najeriya ta yi rashi na daya daga cikin mambobinta, Hon. Muhammad Danjuma Hassan, wanda ke wakiltar mazabar Dawakin Kudu/Warawa a jihar Kano.
Majalisar wakilan ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne a yammacin ranar Juma’a, 10 ga watan Afrilu, 2026, a babban birnin tarayya Abuja, bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya.
An bayyana shi a matsayin daya daga cikin fitattun kwararrun masu tsara dokoki a Najeriya, wanda gudunmawarsa ta taka rawa wajen bunkasa dokoki da tsarin mulki a tsawon shekaru.
Asali: Legit.ng

