Magana Ta Fito: An 'Gano' dalilin Tinubu na Sallamar Ministan Kudi a Najeriya

Magana Ta Fito: An 'Gano' dalilin Tinubu na Sallamar Ministan Kudi a Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya kori ministan kudi Wale Edun a wani sauyi na majalisar ministoci, lamarin da ya ba ‘yan Najeriya mamaki sosai
  • Rahotanni sun nuna rikici tsakanin shugaba da Edun kan jinkirin sakin kudaden kasafin kudi da matsalolin aiwatar da ayyuka, abin da ya jawo suka daga ministoci
  • Sabon minista Taiwo Oyedele ya karbi mukami, yayin da matsin lamba da korafe-korafe suka kara tsananta musamman daga 'yan kwangila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - ‘Yan Najeriya da dama sun yi mamakin labarin da ya fito cewa Shugaba Bola Tinubu ya sallami ministan kudi Wale Edun daga mukaminsa.

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ya fitar ta ce shugaban ya amince da cire Edun tare da ministan gidaje Ahmed Dangiwa.

An samun bayanai kan 'dalilin' korar ministan kudi
Tsohon ministan kudi a Najeriya, Wale Edun da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Rahoto na musamman daga Premium Times ya kawo bayanan silar sabanin da aka samu tsakanin Mai girma Bola Tinubu da Wale Edun.

Kara karanta wannan

2027: Shugaba Tinubu ya ci gaba da sukar 'yan adawa, ya bayyana 'yaudarar' da suke yi

An ji cewa nan take shugaban ya daga darajar karamin ministan kudi Taiwo Oyedele zuwa babban minista.

Yaushe Wale Edun ya zama minista?

An nada Edun a watan Agustan 2023 domin kula da manufofin kudi da tattalin arziki, bayan tsohuwar alakar aiki tsakaninsa da Tinubu tun zamanin mulkin Lagos.

Ko da yake ana kallonsa a matsayin na kusa da shugaban, majiyoyi sun ce an dade ana samun sabani tsakaninsu, musamman kan yadda ake tafiyar da kasafin kudi.

Wannan sabani ya samo asali ne daga korafe-korafe kan jinkirin sakin kudaden ayyukan raya kasa da kuma tangardar tsara kasafin kudi yadda ya kamata.

Matsalar rashin sakin kudaden ayyukan raya kasa ta jawo suka sosai, inda ministoci da ‘yan majalisa suka rika kai korafe-korafe kai tsaye ga shugaban.

Zargin da aka taba yi wa Edun

A watan Fabrairun 2026, ‘yan majalisa sun zargi Edun da rashin aiwatar da kasafin kudin 2025, duk da amincewa da tiriliyan 1.15 domin ayyukan raya kasa.

Sun kuma ce ma’aikatu da hukumomi suna fama da karancin kudi da rashin biyan ‘yan kwangila, lamarin da ya jawo matsin lamba daga bangaren adawa

Kara karanta wannan

Duk da rasa kujerarsa, tsohon minista ya ba da mamaki kan magana game da Tinubu

A nasa bangaren, Edun ya kare kansa da cewa gwamnati ta daina buga kudi ba tare da tsari ba, tana mai mai da hankali kan biyan basussuka.

Ya kuma bayyana cewa kashi 80 cikin 100 na kasafin 2024 an aiwatar da shi, yayin da ake kokarin kammala sakin kudaden 2025 kafin Disamba.

Majiyoyi sun ce shugaban ya yi kokarin sasanta matsalar da tawagar tattalin arziki, amma bai gamsu da bayanan da aka gabatar masa ba.

Ana zargin alaka ta lalace tsakanin Edun da Tinubu
Tsohon ministan kudi da Bola Tinubu ya kora, Wale Edun. Hoto: Federal Ministry of Finance.
Source: Twitter

Cacar baki tsakanin Edun da Tinubu

Rikicin ya kai kololuwa a taron majalisar zartarwa na watan Disamba 2025, inda aka samu cacar baki tsakanin shugaban Najeriya da ministan.

Rahotanni sun ce jami’in tsaron shugaban ya shiga tsakani domin hana Edun daga dagawa shugaban murya a yayin wannan muhawara mai zafi.

Daga wannan lokaci, an fara rage wasu daga cikin ayyukan Edun zuwa ofishin karamin ministan kudi, abin da ya nuna alamun sauyawa.

An ce daga nan ne shugaban ya fara tunanin sauya shi, yayin da ake kallon mukamin a matsayin muhimmin bangare na gwamnati.

Ko da yake Edun ya yi kokarin gyara alaka da shugaban, amma an ce damar samun ganawa da shi ta fara raguwa sosai, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada sababbin ministoci 2 da ya fatattaki Wale Edun da Ahmed Dangiwa

Wani rahoto ya ce har ya je Lagos domin sulhu, amma ganawar da suka yi ba ta kawo karshen rikicin tsakaninsu ba.

'Dalilin Tinubu na korar ministoci 2'

A baya, mun ba ku rahoto cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tsige Ministan kudi, Wale Edun da kuma Ministan gidaje da raya birane, Ahmed Dangiwa.

A lokacin Wale Edun, an samu matsalar raba kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa, inda ma'aikatar lafiya ta samu naira miliyan 36 kacal cikin naira biliyan 218.

Cibiyar bincike da wallafa rahotanni ta ICIR ta bankado wasu manyan dalilai da ta ce su ne suka sanya Tinubu ya tsige ministocin biyu ciki har da matsalar lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.