'Ya Aikata Laifuffuka 9': Kotu Ta Yanke wa Matashi Hukuncin Ɗaurin Shekaru 63
- Wata babbar kotu a Ibadan, jihar Oyo ta yanke wa wani matashi Olaniyan Gbenga Amos hukuncin daurin shekara 63 kan laifin damfara
- Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Amos kan tuhume-tuhume 30 da suka shafi yaudarar jama’a da karyar samun riba daga hannun jari na bogi
- Kotu ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume tara, ta kuma umarce shi da ya biya diyyar kudin da ya karɓa daga hannun wadanda ya damfara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Wata babbar kotu a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta yanke wa wani matashi, Olaniyan Gbenga Amos hukuncin daurin shekaru 63.
Mai shari’a Olusola Adetujoye ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, ya samu Amos da aikata laifin damfara ta hanyar kamfaninsa, Detorrid Heritage Investment.

Asali: Twitter
Bayanin karar da hukumar EFCC ta shigar
Tun da fari, hukumar EFCC ta gurfanar da Amos ne a gaban kotun da ke Ibadan bisa tuhume-tuhume 30 da suka shafi zamba cikin aminci, a cewar sanarwar da ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laifuffukan sun shafi yaudarar jama’a da karyar samun riba, wadanda suka ci karo da sashe na 1(1)(a) da kuma hukunci karkashin sashe na 1(3) na dokar yaudara da damfarar kudi ta 2006.
A cikin takardar tuhumar, EFCC ta bayyana cewa:
“Kai Olaniyan Gbenga Amos da kamfanin Detorrid Heritage Investment Limited, a ranar 18 ga Yuni, 2020, a Ibadan, ka karɓi N995,000 daga Bada Titilope bisa ƙaryar cewa za a saka kudin a kamfanin Crime Alert Security Network tare da alkawarin ba shi ribar kashi 30% cikin makonni 6, duk da ka san hakan ƙarya ce.”
Haka kuma, EFCC ta ce a ranar 29 ga Janairu, 2020, wanda ake karar ya karɓi N920,000 daga wani Onifade Isaac Olawale bisa irin wannan ƙarya da alkawari na boge.
Sai dai bayan da aka gama karanta masa tuhume-tuhume, wanda ake zargin ya musanta aikata dukkanin laifuffukan.
Kotu ta ki wanke matashi daga zargin EFCC
Bayan kotu ta ba da damar fara shari'ar, lauyan EFCC, Sanusi Galadanchi, ya gabatar da shaidu 8 da wasu takardu masu muhimmanci tun a ranar 17 ga Fabrairu, 2022.
Ya kammala gabatar da shaidunsa a ranar 24 ga Janairu, 2023. Daga nan wanda ake zargi ya nemi a wanke shi bisa rashin hujja, amma kotu ta ki amincewa.
Sai dai daga bisani Amos ya gabatar da kansa a matsayin shaida guda tilo domin kare kansa da kuma kamfaninsa. Ya kammala kare kansa a ranar 17 ga Oktoba, 2024.

Asali: UGC
Hukuncin da kotu ta yanke wa matashin
A zaman kotun na ranar Litinin, Mai shari’a Adetujoye ya same shi da laifi a tuhuma ta 6, 16, 17, 18, 19, 21, 22, 23 da 24, kuma ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 7 a kan kowace tuhuma ɗaya.
Amma kotun ta wanke shi daga tuhuma ta 1 zuwa 5, da kuma 7 zuwa 15, da 20, 25 zuwa 30.
Kotu ta ba da umarnin cewa dukkan hukuncin za su gudana a lokaci guda, tare da umarnin Amos ya biya diyyar kudin da ya karɓa ga waɗanda ya yaudara.
Karanta sanarwar a kasa:
Hukuncin daurin shekaru 75 kan Amos
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata kotu a jihar Oyo ƙarƙashin Mai shari’a Bayo Taiwo, ta yanke wa Olaniyan Gbenga Amos hukuncin daurin shekaru 75 kan damfara.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Amos da kamfansa Detorrid Heritage kan tuhume-tuhume guda 35 da suka shafi damfarar wasu mutane Naira biliyan daya.
Mai Shari'a, Taiwo ya yanke wa Amos hukuncin zaman gidan yari na shekara 75 kan laifuka biyar daga cikin 15 da ake tuhumarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng