Yadda Sojoji da Tsohon Minista Suka Raba Miliyoyin Naira don Kifar da Gwamnatin Tinubu
- Gwamnatin tarayya ta zargi tsohon Manjo Janar da wasu da shirin kifar da gwamnati da kuma tallafa wa ta’addanci
- Ana zargin sun raba sama da Naira miliyan 71 domin ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a sassan Najeriya
- Duk da a farkon samun labarin shirya juyin mulkin, gwamnatin tarayya ta ce ƙarya ne kafin a tabbatar a farkon 2025
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin tarayya ta zargi wani tsohon Manjo Janar a rundunar sojin Najeriya, Mohammed Ibrahim Gana, da hannu a wani yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba kan ƙasar.
An shigar da tuhumar ta cikin wata ƙara da aka shigar a kotu mai kwanan wata 20 ga Afrilu, 2026, da babban lauyan kasa kuma Ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi (SAN) ya sanya wa hannu.

Source: Getty Images
Leadership ta wallafa cewa an zargi tsohon janar din da abokan aikinsa da raba sama da Naira miliyan 71 a tsakaninsu domin tallafa wa ayyukan ta’addanci.
Gwamnati ta tafi kotu kan zargin juyin mulki
Premium Times ta wallafa cewa a cikin takardar tuhuma mai lamba FHC/ABJ/CR/206/2026, an ambaci wasu da ake zargi.
Daga ciki har da tsohon Kyaftin na rundunar ruwa Erasmus Victor, Sufeta Ahmed Ibrahim, Zekeri Umoru, Bukar Goni da Abdulkadir Sani.
Haka kuma, an ambaci tsohon karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, wanda ake zargin yanzu haka baya kasar.
Gwamnatin ta zargi waɗannan mutane da laifuffuka da suka haɗa da cin amanar ƙasa, ta’addanci, ɓoye bayanan tsaro da kuma safarar kuɗaɗen da ake dangantawa da ta’addanci.
Ana zargin sun haɗa kai a shekarar 2025 domin tayar da yaƙi kan ƙasa da nufin hambarar da Shugaban Ƙasa,” laifi da dokar ƙasa ta tanadar da hukunci a kansa.

Kara karanta wannan
Za a kai wadanda suka shirya yi wa Tinubu juyin mulki kotu, an jero laifuffukansu
Haka kuma ana zargin sun san da wani shirin cin amanar ƙasa da wasu ke shiryawa amma suka kasa sanar da hukumomi.
An gano makircin kifar da gwamnatin Tinubu
Baya ga zargin cin amanar ƙasa, ana tuhumar waɗanda ake zargin da haɗa baki wajen aikata ta’addanci ƙarƙashin dokar hana ta’addanci ta 2022.
An ce wasu daga cikinsu sun halarci taruka domin ciyar da wata akidar siyasa gaba wadda za ta iya girgiza tsarin mulkin Najeriya.
Haka kuma ana zarginsu da bayar da tallafi kai tsaye ko a fakaice domin sauƙaƙa ayyukan ta’addanci.
A cewar masu gabatar da ƙara, waɗannan mutane sun ɓoye muhimman bayanan sirri da za su taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci amma suka kasa sanar da hukumomin da suka dace a kan lokaci.

Source: Twitter
Takardun kotu sun kuma nuna cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargi sun karɓi kuɗi masu yawa da ake zargin na tallafin ta’addanci ne, ciki har da Naira miliyan 50, Naira miliyan 10 da sauransu.
A baya, rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin juyin mulki a watan Oktoba 2025, tana mai cewa kama wasu jami’ai 16 ya shafi ladabtarwa ne kawai.

Kara karanta wannan
Saraki ya jefi gwamnatin Buhari da zargi kan fashin Offa, ya fallasa gwamnan Kwara
Sai dai a watan Janairu 2026, rundunar ta tabbatar da cewa bincike ya gano wani shirin juyin mulki, wanda ake zargin ya haɗa da tayar da hankali yayin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, tare da kama manyan jami’an gwamnati da na soji.
Gwamnatin Najeriya ta shigar da tuhume-tuhume 13
A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin tarayya ta shigar da tuhume-tuhume guda 13 a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan wasu da ake zargi da yunkurin juyin mulki.
Daga cikin wadanda ake zargin akwai wani tsohon Manjo Janar, tsohon Kyaftin na rundunar sojin ruwa, wani jami’in ‘yan sanda mai babban mukami a Najeriya.
Ana zargin wadanda ake tuhumar da laifin yaki da Najeriya da kuma aikata laifuffukan da suka shafi cin amanar kasa da ta’addanci, yunkurin juyin mulki a sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
