'Yan Bindiga Sun Sace Basarake cikin Dare, an Shiga Daji Farautar 'Yan Ta'addan
- Wasu ’yan bindiga sun sace dagacin kauyen Dickson Idu a farmaki da suka kai da yamma a karamar hukumar Ohimini ta jihar Benue
- Dakarun soji da ’yan sanda da jami’an tsaron farar hula sun fara bincike da sintiri don gano inda aka boye dagacin a cikin daji
- A wani farmaki na daban, rundunar ’yan sanda ta hallaka wani babban dan bindiga da ya addabi yankin Zaki-Biam na jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace dagacin wani kauye mai suna Dickson Idu, mai shekaru 50 a jihar Benue, cikin daren Litinin, 29 ga watan Afrilu, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30 na dare a wani titin da ke cikin daji tsakanin kauyukan Egwanokwu da Aiegaji da ke karamar hukumar Ohimini.

Asali: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce tuni jami’an tsaro suka fara daukar mataki, ciki har da dakarun soji, ’yan sanda da jami’an tsaron farar hula na jihar, domin ceto basaraken.
Jami’an tsaro sun bazama neman basaraken
Tun bayan samun rahoton sace dagacin, hukumomi sun bazama cikin dazuka domin neman inda aka boye shi tare da kokarin ganin an ceto shi ba tare da wani lahani ba.
Wata majiya ta tsaro ta shaida cewa ana amfani da fasahar gano bayanai da kuma hadin gwiwar al’ummar yankin don zakulo inda barayin suka nufa.
Ana sa ran rundunar hadin gwiwar za ta cigaba da sintiri ba dare ba rana, domin ceto rayuwar dagacin da kama 'yan ta'addan da suka sace shi.
An hallaka fitaccen dan bindiga a Benue
A wani farmakin, rundunar ’yan sanda ta jihar Benue ta ce ta kashe wani sanannen dan bindiga da ya dade yana addabar yankin Zaki-Biam mai suna Akumave Shogodo.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar 29 ga Afrilu, da misalin karfe 6:30 na safe, bayan samun bayanan sirri kan maboyar ’yan ta’addan.
Bayanai sun nuna cewa da isar jami’an tsaro wajen, 'yan bindigan suka bude wuta. Hakan ya haddasa musayar wuta, inda rundunar ta yi amfani da makamai masu karfi wajen fatattakar su.

Asali: Facebook
Akumave Shogodo ya samu rauni mai tsanani a musayar wutar kuma aka garzaya da shi asibiti, inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.
Rundunar ta ce ta kwato bindiga kirar gida daga hannunsa, yayin da sauran miyagun suka tsere da raunuka daban-daban.
'Yan bindiga sun sace basarake a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun shiga gidan wani basarake a jihar Kaduna da ke Arewa ta Yamma.
An ruwaito cewa 'yan bindigar sun sace matar basaraken tare da wata 'yar shi a harin da suka kai cikin dare.
Mutanen yankin sun yi kokarin ceto matan da aka sace, amma sai dai 'yan bindigan sun harbi mutum daya daga cikinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng