Sauya Sheka: Kwankwaso Ya Jawo wa Ganduje Rasa Mogoya Baya a Abuja

Sauya Sheka: Kwankwaso Ya Jawo wa Ganduje Rasa Mogoya Baya a Abuja

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi wasu fitattun ’yan siyasa daga jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa NNPP a gidansa dake Abuja
  • Sababbin mambobin sun fito daga kananan hukumomi daban-daban na jihar Kano, kuma sun bayyana goyon bayansu ga tafiyar Kwankwasiyya
  • Baya ga haka, Kwankwaso ya kuma gana da Jakadan Tarayyar Turai kan ci gaban tattalin arziki da karfafa dimokuradiyya a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karbi wasu jiga-jigan APC da suka sauya sheka zuwa jam’iyyarsu.

Taron karbar sababbin mambobin ya gudana ne a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025, a gidan Sanata Rabiu Kwankwaso da ke Abuja, inda aka karbi mambobin cikin farin ciki.

Kwankwaso
Kwankwaso ya karbi 'yan APC zuwa NNPP. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan sauya shekar ne a cikin wani sako da hadimin Sanata Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya bayyana jin dadinsa da ganin irin wadannan mutane masu kima da tasiri sun rungumi tafiyar NNPP da Kwankwasiyya.,

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi masu sauya shekar ne a daidai lokacin da ake rade radin zai koma jam'iyya mai mulki a Najeriya.

Sunayen 'yan APC da suka koma NNPP

Cikin sababbin mambobin da suka sauya sheka zuwa NNPP akwai Alhaji Zahradeeni Yusuf daga karamar hukumar Gwarzo da Alhaji Bello Usman daga karamar hukumar Gwale,

Haka zalika daga cikinsu akwai Injiniya Ahmad Muhammad daga da ya fito daga karamar hukumar Kura a jihar Kano.

Kwankwaso ya yaba da jajircewar wadannan mutane wajen hakuri da sauyin siyasa, yana mai cewa jam’iyyar NNPP za ta ci gaba da karbar duk wanda ke da muradin inganta Najeriya.

Mabiya akidar Kwankwasiyya a kafar sada zumunta ta Facebook sun nuna farin ciki da sauya shekar da mutanen suka yi zuwa APC.

Kwankwaso ya gana da Jakadan Tarayyar Turai

A wani bangare kuma, a ranar Talata 29 ga Afrilu, 2025, Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi bakuncin Jakadan Tarayyar Turai, Gautier Mignot, a gidansa dake Abuja.

Yayin ganawar, shugabannin sun tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arziki da dorewar dimokuradiyya.

Kwankwaso
Kwankwaso ya gana da jakadan tarayyar Turai a Abuja. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Tattaunawar ta maida hankali kan irin rawar da za a iya takawa wajen inganta ci gaba mai dorewa, zuba jari, da kuma karfafa tsarin shugabanci nagari a Najeriya da kasashen Afrika.

Ana ganin tafiyar siyasar Kwankwaso ta mayar da hankali ne kan samar da shugabanci na gari, zuba jari a bangarorin da suka fi shafar rayuwar jama’a kamar ilimi, lafiya da cigaban matasa.

Tafiyar Kwankwasiyya a yanzu

A halin yanzu, tafiyar siyasar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ke karkashin tutar Kwankwasiyya a jihar Kano na fuskantar wasu kalubale, musamman sakamakon barin wasu matasa da suka dade cikin tafiyar.

Ko da yake a kwanan nan Kwankwaso ya karɓi wasu fitattun ’yan siyasa daga jam’iyyar APC zuwa NNPP a gidansa dake Abuja, akwai alamun cewa akwai wasu daga cikin matasan Kwankwasiyya da ke nuna rashin gamsuwa da tafiyar a yanzu.

Wasu daga cikinsu na ganin cewa tafiyar na fuskantar raguwa wajen jawo hankalin matasa da sauransu, musamman ganin rade-radin cewa Kwankwaso zai iya komawa jam’iyyar da ke mulki.

A gefe guda, shugabancin Kwankwaso ya ci gaba da neman goyon baya ta hanyar karɓar sababbin mambobi daga sassa daban-daban na Kano, kamar yadda aka gani da shigar Alhaji Zahradeeni Yusuf daga Gwarzo da sauran su.

Amma hakan bai hana fuskantar matsalolin da suka shafi rikice-rikicen cikin gida ba. Yayin da yake kokarin farfado da Kwankwasiyya, dole ne Kwankwaso ya duba dalilan da ke sa matasa ke barin tafiyar domin a daidaita tsarin cikin gida da sake gina karfin hadin kai tsakanin mambobi.

Ganduje ya ce 'yan adawa za su koma APC

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdulahi Umar Ganduje ya ce wasu jagororin adawa na shirin komawa APC.

Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa akwai wasu daga cikin gwamnonin PDP da ke shirin komawa jam'iyyar APC a nan gaba kadan.

Ganduje ya fadi haka ne a wani taron da APC ta shirya a jihar Delta domin karbar gwamnan jihar da ya sauya sheka zuwa APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng