Kasar Iran Ta Gindaya Sharuɗan Sake Zama a Teburin Tattaunawa da Amurka
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi magana game da sake dawowa kan teburin tattaunawa da kasar Amurka da ake shirin yi
- Iran ta ce za ta dawo teburin tattaunawa ne kawai idan Amurka ta kawo karshen shingen jiragen ruwa da ta kakaba a mashigar Hormuz
- Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya ce Amurka na karya yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma dole ta dakatar da hakan kafin a ci gaba da sulhu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - A wani muhimmin lamari na diflomasiyya, Iran ta bayyana sharadi kafin dawo da tattaunawa da Amurka.
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya ce za su tattauna ne idan Amurka ta kawo karshen shingen jiragen ruwa.

Source: Facebook
Rahoton The Economic Times ya ce Iravani ya bayyana cewa wannan shinge na Amurka ya karya yarjejeniyar tsagaita wuta da ake ta kokarin samarwa a tsakanini kasashen biyu.
Mashigar Hormuz: Donald Trump ya zargi Iran da karya
Hakan na zuwa ne yayin da Donald Trump ke yin zargi mai karfi ga Iran musamman game da mashigar Hormuz da ake ta takaddama kanta.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran na boye gaskiya, yana mai zargin cewa a sirrance tana neman bude mashigar Hormuz saboda asarar kusan dala miliyan 500 kullum.
Trump ya ce rufe mashigar na matukar illata tattalin arzikin Iran, duk da cewa a fili tana nuna tsayin daka kan rikicin domin dalilan siyasa ga jama’a, cewar Middle East Monitor.
A halin yanzu, tashin hankali na kara kamari bayan rahoton cewa wani jirgin ruwa ya samu mummunar lalacewa bayan harin da jirgin IRGC ya kai kusa da Oman.
Mashigar Hormuz na da matukar muhimmanci ga kasuwannin mai da iskar gas na duniya, kuma rikicin da ke faruwa a yankin na barazana ga tsaron jiragen ruwa da tattalin arzikin duniya baki daya.

Source: Twitter
Sharadin Iran ga Amurka kafin sake tattaunawa
Iravani ya bayyana cewa dole ne Washington ta dakatar da hakan kafin fara sabon zagayen tattaunawa a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Ya ce:
“Ba mu fara yaki ba, su ne suka fara. Idan suna son sulhu, za su same mu a shirye, idan kuma yaki suke so, mu ma a shirye muke.”
Maganganun nasa sun nuna cewa duk da akwai damar tattaunawa, cire wannan shinge shi ne babban cikas, yana kara nuna rashin amincewa tsakanin kasashen biyu duk da tsawaita tsagaita wuta.
Kawayen Iran na barazanar rufe wata mashiga
An ji cewa wani jami’i a gwamnatin ‘yan Houthis ya yi barazanar rufe mashigar Bab al-Mandeb idan manufofin Shugaban Amurka, Donald Trump suka ci gaba.
Hussein al-Ezzi ya ce idan Sanaa ta rufe mashigar, babu wanda zai iya sake bude ta, yana kira a dakatar da manufofin da ke hana zaman lafiya.
Mashigar Bab al-Mandeb hanya ce mai muhimmanci ga kasuwancin duniya, tana hada Tekun Ja da Gulf of Aden tare da saukaka zirga-zirgar mai da kaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

