"Ɗan Arewa kaɗai," Dele Momodu Ya Faɗi Wanda Zai Iya Kayar da Shugaba Tinubu a 2027
- Dele Momodu ya ce duk wani ɗan Kudu da ke shirin neman kara wa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ɓata lokacinsa kawai yake yi
- Fitaccen ɗan jaridar ya bayyana cewa babu wani ɗan takara da zai iya gwabzawa da Tinubu a zaɓen 2027kuma ya yi nasara sai ɗan Arewa
- Jigon na jam'iyyar PDP ya ce galibin shugabannin al'umma daga Kudancin Najeriya suna goyon bayan tazarcen Shugaba Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Fitaccen ɗan jarida kuma jigo a jam’iyyar PDP, Cif Dele Momodu, ya bayyana cewa dan takara daga Arewacin Najeriya ne kaɗai zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Momodu, wanda ya taɓa neman tsayawa takarar shugaban kasa ya ce idan har ana son kayar da Shugaba Tinubu, dole a lalubo ɗan takara daga Arewa a mara masa baya.

Asali: Facebook
Jigon na PDP ya faɗi haka ne wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise News a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane ɗan takara zai iya kayar da Tinubu?
Momodu ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa daga Kudancin Najeriya da zai iya doke Tinubu, wanda ake sa ran zai nemi wa’adin mulki na biyu a zaɓe mai zuwa.
“Ina da wata dabara mai sauƙi, babu wanda zai iya ja da Tinubu a wannan karon sai ɗan Arewa. Duk wani dan Kudu da ke cewa zai ƙwace mulki daga hannun Tinubu, to yana bata lokaci ne kawai.”
Dele Momodu ya ce Tinubu ya nuna sha'awar neman tazarce kuma da dama daga cikin shugabannin Kudu suna goyon bayansa, Tribune Nigeria ta kawo.
“Tinubu ba ya son barin kujerar mulki, burinsa ya zarce wa'adi na biyu. Mutanen Kudu ma sun ce suna so ya ci gaba,’” in ji shi.
Dele Momodu ya gargaɗi mutanen Kudu
Sai dai Momodu ya yi gargaɗi cewa kiran tazarcen Tinubu a matsayin “shirin Kudu” zai iya jawo hatsaniya da tayar da jijiyar wuya daga sauran yankuna, musamman Arewa.
“Mun yi wannan kuskuren a 'June 12'. Mun maida amanar kasa da aka bai wa Abiola ta zama ta kabilar Yarbawa. Irin wannan kuskuren nake ganin mutanen Tinubu na shirin maimaitawa yanzu.
“Idan ka duba tsarin ministocinsa, mutane na cewa ya naɗa Yarbawa ne saboda kabilarsa ce, amma lamarin ba haka yake ba, abokansa kaɗai yake naɗa wa," in ji shi.

Asali: Twitter
Ɗan Arewa ne kaɗai zai iya karawa da Tinubu
Momodu ya jaddada cewa jam'iyyar PDP ko haɗakar ƴan adawa za su samu nasarar karɓe mulki daga hannun Tinubu ne idan sun tsayar da ɗan Arewa takara.
Ya ce:
“Na ji labarin wani daga yankin Yarbawa na shirin fitowa takara, na san a ƙarshe hakan ba zai taɓa yiwuwa ba don ba zai iya da Shugaba Tinubu ba.
Wani masoyin Atiku kuma ɗan PDP, Kabiru Dogo ya ce wannan magana ta Dele Momodu gaskiya ce, babu wanda zai iya kayar da Tinubu a yadda abubuwa ke tafiya sai ɗan Arewa.
Ɗan siyasar ya shaidawa Legit Hausa cewa a ganinsa, kamata ya yi manyan ƴan siyasar Arewa su haɗa kai wuri guda su tsaida mutum ɗaya.
"Abu ne mai wahala kayar da Tinubu a 2027, hanya ɗaya ce nake gani kuma ita ce manyan Arewa su haɗu su marawa mutum ɗaya baya, idan ba haka ba, Tinubu ya ci zaɓe ya gama."
Tinubu ya samu goyon bayan sarakunan Ibo
A wani labarin, kun ji cewa sarakunan Ibo a Najeriya sun sha alwashin marawa Shugaba Bola Tinubu baya a babban zaɓen 2027.
Sarakunan gargajiyar sun yi alƙawarin bai wa Tinubu ƙuri'a mafi tsoka na mutanen yankinsu a zaɓe mai zuwa domin ya yi tazarce wa'adi na biyu.
Ƙungiyar sarakunan ta bayyana wannan matsaya ne ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Eze Nnamdi Oforegbu daga jihar Abia.
Asali: Legit.ng