Dele Momodu Ya Fallasa yadda Wike Ya Yi Silar Ficewar Peter Obi daga PDP

Dele Momodu Ya Fallasa yadda Wike Ya Yi Silar Ficewar Peter Obi daga PDP

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Dele Momodu, ya yi tone-tone kan abubuwan da suka faru a PDP kafin zaɓen 2023
  • Dele Momodu ya zargi ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da yin silar ficewar Peter Obi daga jam'iyyar PDP
  • Jigon na PDP ya bayyana cewa Wike ya yi silar ficewar Peter Obi ne domin ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya nuna yatsa ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Dele Momodu ya zargi Nyesom Wike da yin silar ficewar Peter Obi daga jam’iyyar PDP.

Wike da Peter Obi
Dele Momodu ya ce Wike ne ya yi silar ficewar Peter Obi daga PDP Hoto: @PeterObi, @Govwike
Asali: Facebook

Yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise tv a ranar Laraba, Dele Momodu ya ce Wike ne sanadiyyar ficewar Peter Obi daga jam’iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin shirin babban zaɓen 2023, Peter Obi ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar LP, inda ya fito takarar shugaban ƙasa.

Me Dele Momodu ya ce kan Nyesom Wike

Ya bayyana cewa kafin zaɓen 2023, Atiku Abubakar yana son jam’iyyar PDP ta miƙa mulki zuwa yankin Kudu maso Gabas maimakon ci gaba da juyawa tsakanin wasu yankuna.

Jigon na PDP ya nuna cewa da Wike bai nesanta kansa da yankin Kudu maso Gabas ba, da zai iya amfana daga wannan shawarar da Atiku ya ba da.

A cewar Dele Momodu, Wike ya cire kansa da kansa daga jerin ƴan takara saboda ya bayyana cewa shi ba Ibo ba ne.

Ya ƙara da cewa tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce ba ya da wata alaƙa da manufar Ibo.

Tun da PDP na la'akarin bai wa yankin Kudu maso Gabas tikitin shugaban ƙasa, Momodu ya yi zargin cewa Wike ya yi silar ficewar Peter Obi domin samun tikitin jam’iyyar.

Dele Momodu
Dele Momodu ya nuna yatsa ga Wike Hoto: Dele Momodu
Asali: UGC

Yadda Wike ya jawo Peter Obi ya bar PDP

"Mutanen Wike ne da ke ƙorafi kan Arewa da Kudu suka kawo kwamitin da ya ce a bar kowa ya shiga zaɓen fidda gwanin jam'iyyarmu."
"Hakan ya sanya na samu damar sayan fam. Na saya fam a wancan lokacin saboda Atiku ya gaya musu cewa idan suka bar mulki zuwa yankin Kudu maso Gabas, hakan ya yi masa daidai, amma idan za a bari ne a riƙa ƙarba-ƙarba tsakanin wasu ƴan ƙalilan yankuna, ba zai goyi baya ba."
"Yana son su bari mulki ya je Kudu maso Gabas. Amma saboda Wike ya riga da kori kansa ta hanyar cewa shi ba Igbo ba ne, shi ɗan Kudu maso Kudu ne, ba ruwan shi da wani abu da ya shafi Igbo, sai ya yi silar ficewar Peter Obi jam'iyyar. Ta yadda zai samu damar takara."

- Dele Momodu

Momodu ya magantu kan komawar Atiku APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya musanta batun cewa Atiku Abubakar zai koma APC.

Dele Momodu ya bayyana cewa batun Atiku zai koma jam'iyyar APC abu ne wanda ba zai taɓa yiwuwa ba.

Ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan ba ya neman mulkin Najeriya ko ta halin ƙaƙa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng