Sarakunan Gargajiya da Gwamnoni Suka Dakatar a 2025 kan Zarge Zarge Mabambanta

Sarakunan Gargajiya da Gwamnoni Suka Dakatar a 2025 kan Zarge Zarge Mabambanta

  • Wasu gwamnoni sun dakatar da sarakunan jihohinsu tun daga watan Janairu 2025 zuwa yanzu saboda zarge-zarge kamar cin hanci da rashin adalci
  • A jihar Ogun, Oba Abdulsemiu Ogunjobi ya fuskanci dakatarwa bisa cin zarafin wani dattijo mai shekaru 73, lamarin da ya jawo abin tir da Allah wadai
  • Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya dakatar da sarakuna da dama, ciki har da Sarkin Daware, saboda cin hanci, kwace filaye da barazana ga zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Wasu gwamnoni a Najeriya sun dauki mataki kan sarakunan gargajiya a jihohinsu saboda zarge-zarge.

An dakatar da mafi yawan sarakunan ne daga karagar mulki duba da girman laifuffukan da suka aikata.

Jerin gwamnonin da suka dakatar da sarakuna a jihohinsu
Sarakunan gargajiya da gwamnoni suka dakatar a 2025. Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri, Bassey Otu, Rt. Hon. Monday Okpebholo.
Asali: Facebook

Sarakuna da gwamnoni suka dakatar a 2025

Daga cikin zarge-zargen da ake yi wa sarakunan da aka dakatar akwai kwacen filaye da cin hanci da rashawa, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran laifuffukan sun hada da rashin jagoranci nagari da cin zarafin al'umma da ke karkashinsu da sauransu.

Tun farkon wannan shekara ta 2025 tun daga watan Janairu zuwa yanzu da muke karshen watan Mayu, an dakatar da sarakuna da dama.

Legit Hausa ta duba wasu daga cikin sarakunan da gwamnoni suka dakatar a wannan shekara ta 2025.

1. Bassey Otu - Cross River

Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu, ya amince da dakatar da Hakimin Esuk Utan, Cif Okon Archibong, tare da majalisarsa nan take.

Dakatarwar ta biyo bayan zarge-zargen amfani da ofis ba bisa ka’ida ba, wanda ya jawo korafe-korafe da dama daga mazauna yankin.

Gwamnatin jihar ta ce akwai zarge-zarge masu yawa da aka gabatar kan yadda Cif Okon Archibong, da majalisarsa ke tafiyar da al’amuran yankin.

Gwamna ya dakatar da basarake kan zarge-zarge
Yawan sarakunan gargajiya da gwamnoni suka dakatar a 2025. Hoto: Hon. Bassey Otu.
Asali: Facebook

2. Dapo Abiodun - Ogun

Gwamnatin Jihar Ogun ta dakatar da Olorile na Orile Ifo, Oba Abdulsemiu Ogunjobi har tsawon watanni shida bisa cin zarafin wani dattijo mai shekaru 73.

Gwamna Dapo Abiodun ya dauki matakin ne bayan basaraken ya ci zarafin dattijon mai suna Cif Abraham Areola.

Hakan ya biyo bayan yada wani bidiyo na tsawon minti biyu a kafafen sada zumunta, inda Oba ya la’anci dattijon da iyalinsa bisa zargin hada baki akansa.

3. Ahmadu Umaru Fintiri - Adamawa

A watan Faburairun 2025, Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya kori dukkan hakimai da masu rike da sarautun gargajiya a yankunan sababbin masarautun da ya ƙirƙiro.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a garin Gulak, yayin da yake mika sandar mulki ga sabon sarkin Madagali, Ali Danburam, Premium Times ta ruwaito.

A cikin watan Disambar 2024, Gwamna Fintiri ya kafa sababbin masarautu guda bakwai, wanda hakan ya sa jimillar masarautun gargajiya a jihar suka kai 14.

Gwamna Fintiri ya dakatar da basarake
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya dakatar da Sarkin Daware a Adamawa. Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri.
Asali: Facebook

4. Monday Okpebholo - Edo

Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da babban basarake kan garkuwa da mutane da ya addabi al'ummar yankin a kwanakin nan.

Gwamna Okpebholo ya dakatar da Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode a karamar hukumar Etsako ta Gabas, George Egabor nan take.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun kama Sakataren sarkin, Peter Omiogbemhi, bayan wani lamari da ya hallaka dattijon fada, John Ikhamate.

Gwamna ya dakatar da Sarki kan rashin tsaro
Wasu daga sarakunan gargajiya da gwamnoni suka dakatar a 2025. Hoto: Rt. Hon. Monday Okpebholo.
Asali: Twitter

5. Ahmadu Umaru Fintiri - Adamawa

A baya bayan nan, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya dakatar da Sarkin Daware, Alhaji Hassan Ja’afaru kan zargin cin hanci da gazawar shugabanci.

A cikin wata sanarwa da aka fitar, an umarci basaraken da ya yi gaggawar mika duk kadarorin gwamnati dake hannunsa ga wanda ya dace.

Majiyoyi sun ce ana zargin Ja’afaru da laifin kwace gonaki, kin zama cikin masarautarsa da kuma barazana ga zaman lafiya a yankin.

Gwamna Fintiri ya sha alwashin cewa ba zai kyale kowa ba wajen yaki da cin hanci da rashawa a fadin jihar Adamawa.

Sarakuna da kotu ta tsige a shekara 1

A baya, kun ji cewa sarakunan gargajiya a Najeriya na da tasiri sosai a cikin al’umma duba da mutuncin da suke da shi.

Amma abubuwan da ke faruwa sun sa wasu ‘yan kasa fara shakkun ƙarfinsu duba da cewa yanzu makomar sarakuna na kara komawa hannun ƴan siyasa da kotuna.

A shekara guda da ta gabata ta 2024, akalla masu martaba biyar suka rasa sarautarsu wanda ke kara tabbatar da darajarsu na raguwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.