2027: Minista a Gwamnatin Marigayi Buhari Ya Ayyana Neman Takarar Gwamna
- Tsohon ministan makamashi a mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari zai nemi takarar gwamna a zaben shekara mai zuwa
- Sale Mamman ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a shekarar 2027 da ake tunkara wanda ake ganin zaben zai dauki hankulan al'umma
- Ya ce ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi 16, yana kira ga jama’a su rungumi shugabanci mai tsari da manufofi masu kyau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jalingo, Taraba - Tsohon ministan makamashi a mulkin marigayi Muhammadu Buhari zai nemi takarar gwamna a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Injiniya Sale Mamman, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Taraba a zaben 2027 da ake tunkara domin kawo sauyi.

Source: Facebook
Mamman ya bayyana haka ne yayin da ya ke jawabi ga dimbin magoya baya a ofishin yakin neman zabensa a Jalingo a karshen mako, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan
"Wasun su hotiho ne": Tsohon dan majalisa ya gargadi Tinubu kan dogaro da gwamnoni a 2027
Matakan da Sale Mamman ke bi a siyasance
Mamman ya ce ya riga ya fara gudanar da tuntuba mai fadi da masu ruwa da tsaki a dukkan kananan hukumomi 16 na Taraba, domin shiryawa tsaf don zaben 2027 mai zuwa.
Ya bukaci al’ummar jihar su kasance masu hakuri tare da rungumar salon shugabanci mai maida hankali kan manufofi masu inganci da kuma auna sahihin ci gaban da za a samu.
Ya nuna damuwa kan gibin da ake da shi a bangaren ababen more rayuwa, shugabanci da ci gaban tattalin arziki, yana mai cewa Taraba ta yi baya idan aka kwatanta da jihohin da aka kirkire su tare.
Ya ce:
“An kirkiri Taraba shekaru 34 da suka gabata, amma har yanzu muna baya wajen samar da ababen more rayuwa, ciki har da hanyoyi masu kyau a birni da karkara."

Source: Original
'Musabbabin rashin samun ababan more rayuwa a Taraba'
Ya kara da cewa rashin ci gaban ya samo asali ne daga rashin kyakkyawan shugabanci, wanda ya haifar da rashin samar da muhimman abubuwan more rayuwa da al’umma ke bukata matuka.
Tsohon ministan ya ce dawowarsa siyasa ta samu ne sakamakon kiraye-kirayen da ya samu daga jama’a da masu ruwa da tsaki, wadanda suka yarda da kwarewarsa wajen farfado da jihar.
Haka kuma ya bayyana muhimman bangarori da ke bukatar kulawa cikin gaggawa, da suka hada da hanyoyi, noma, ilimi, tsaro da tattalin arziki, yana cewa shugabanci nagari ne kadai zai bude damarmaki ga Taraba, cewar rahoton Leadership.
Ministan Tinubu zai nemi takarar gwamnan Oyo
Mun ba ku labarin cewa ministan makamashin Najeriya, Bayo Adelabu, ya fito fili ya jaddada kudirinsa na shiga tseren takarar gwamnan Oyo a 2027.
Mista Adebayo Adelabu ya bayyana cewa ya bi matakai da dama na neman gwamnan tun 2019 kuma lokaci ya yi da zai mulki Oyo domin kawo ci gaba da inganta rayuwar al'umma.
Ya yi amfani da kalmar “Emi lokan” wadda ke nufin “Lokaci na ne” da Bola Tinubu ya yi amfani da ita a lokacin yakin zabensa domin tabbatar da cewa shi ma lokacinsa ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
