Yadda Takaita Intanet na Kwanaki 54 a Iran ke Jawo Asara

Yadda Takaita Intanet na Kwanaki 54 a Iran ke Jawo Asara

  • An shafe kwanaki 54 ana takaita intanet a Iran tun bayan fara yaƙin Gabas da Tsakiya da Amurka da Isra'ila suka takalo
  • Takunkumin ya biyo bayan zanga-zangar adawa da gwamnati da wasu ke shirya wa da kuma rikicin Amurka da Isra’ila
  • Tsawon kwanakin da aka shafe babu cikakken aiki da intanet ya fara jefa wasu bangarori na ci gaba a cikin gagarumar matsala

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Iran – Kungiyar sa ido kan harkokin intanet ta NetBlocks, ta bayyana damuwa a kan yadda aka shafe kusan kwanaki 54 ana tsaurara matakan amfani da intanet a Iran.

Kungiyar ta ce tun bayan da aka fara yaƙin Amurka da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya, mahukunta a Iran suka katse ko takaita intanet, kuma an shafe sama da awanni 1,272 a haka.

Kara karanta wannan

Iran na ƙara ɗaura ɗamarar yaƙi, ta ce ba za ta lamunci 'zaluncin' Amurka ba

Har yanzu ba a dawo amfani da cikakken intanet a Iran ba
Shugaban jamhuriyar Musulunci ta Iran Masoud Pezeshkian Hoto: Anadolu Ajansi
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta wallafa cewa rahoton ya bayyana cewa wannan yanayi na katsewar intanet ya zama daya daga cikin mafi tsawo da aka taba gani a kasar cikin ‘yan shekarun nan.

Iran: An shiga damuwa kan takaita intanet

Iran International ta ruwaito takaita intanet a wasu wurare tare da katse shi a wasu yankunan a Iran ya kara jawo damuwa daga kungiyoyin kare ‘yancin jama’a da masu sa ido kan harkokin sadarwa a duniya.

Takunkumin ya fara ne bayan sake barkewar zanga-zangar adawa da gwamnati a farkon watan Janairu na shekarar 2026 da aka fara.

Daga bisani, matakan suka kara tsananta bayan barkewar rikici tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran a karshen watan Fabrairu na shekarar 2026.

Takaita intanet na shafar tattalin arzikin Iran

Masana sun ce tsauraran matakan takaita intanet sun yi matukar tasiri ga rayuwar yau da kullum da kuma tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

"Abu 1 muke tsoro," Qatar ta tsoma baki kan batun tattaunawar sulhun Amurka da Iran

'Yan kasuwa, musamman masu dogaro da intanet wajen gudanar da harkokinsu, sun fuskanci tsaiko da asarar kudin shiga masu tarin yawa.

Haka zalika, ma’aikata da dama da ke aiki ta hanyar intanet sun kasa gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, lamarin da ya haifar da koma baya a bangarori da dama na tattalin arziki.

An Katse intanet tun farkon yakin Amurka da Isra'ila a Iran
Masoud Pezeshkian, shugaban kasar Iran Hoto: Masoud Pezeshkian
Source: Getty Images

Kungiyoyi masu zaman kansu da ke sa ido kan harkokin sadarwa sun yi gargadin cewa irin wannan tsauraran mataki na iya kara dagula al’amura, musamman idan aka yi la’akari da yadda tattalin arzikin duniya ke kara komawa kan fasahar zamani.

Har ila yau, akwai fargabar cewa ci gaba da takaita intanet na iya kara tsananta rashin jin dadin jama’a, musamman a daidai lokacin da ake fama da rikice-rikicen siyasa da na tsaro a cikin kasar.

Donald Trump ya yi wa Iran barazana

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce dole ne Iran ta shiga tattaunawa ko ta fuskanci matsaloli da ba a taɓa ganin irinsu ba.

Ya jaddada cewa Amurka ba za ta amince Iran ta mallaki makamin nukiliya ba ko ana cikin wane irin yanayi, kuma hakan ginshiki ne a batun sulhu da ake yi.

Trump na wannan barazana bayan Iran ta nuna rashin yarda da Amurka da aka yi zargin ta karya yarjejeniyar da aka cimma ta hanyar kai wa jirginta hari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng